Yadda Tinubu Ya Ba Hadimin Buhari Mukami a Kasar Turai domin Rufe Bakin Bakin Shi

Yadda Tinubu Ya Ba Hadimin Buhari Mukami a Kasar Turai domin Rufe Bakin Bakin Shi

  • Godswill Akpabio ya nuna shi ne ya shiga ya fita har Ita Enang ya samu kujerar ambasada zuwa ƙasar Jamus
  • Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon sanatan cikin jakadun Najeriya a ƙasashen ƙetare
  • Shugaban Majalisar dattawa ya ce saboda sukar da yake yi wa gwamnan Akwa Ibom aka ba shi kujerar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Akwa Ibom - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce ya taka rawa wajen ba Ita Enang muƙamin jakadanci.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta naɗa tsohon Sanatan Akwa Ibom, Ita Enang a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Jamus.

Godswill Obot Akpabio
Shugaban majalisa, gwamna Umo Eno da wasu manya wajen yi wa APC addu'a a coci a Akwa Ibom Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Gwamnati ta rufe wa Sanata Ita Enang baki

Premium Times ta rahoto cewa an yi hakan ne domin ya dakatar da sukar da yake yi wa Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.

Godswill Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron addu'a na musamman da aka yi domin APC.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fallasa danyen aikin da Buhari ya yi da ya bar Tinubu da wahala

An gudanar da addu’o’i na musamman domin kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar APC na 2027 a jihar Akwa Ibom.

Da yake ba da labarin wata tattaunawa da ya yi da Ita Enang, 'dan siyasar ya ce ya shiga tsakaninsu da gwamnan Akwa Ibom.

Yadda Godswill Akpabio suka yi da Ita Enang

Shugaban majalisar dattawan ya lura cewa tsohon sanatan yana ta sukar gwamnatin Umo Eno duk da suna jam’iyya guda.

Akpabio ya ce:

“A cikinmu akwai wani mutum da ya shahara wajen sukar gwamnatocin baya a Akwa Ibom.
Amma wata rana na kira shi, na ce masa, wannan Fasto Umo Eno da Ubangiji ya ba mu, don Allah ka daina zaginsa.”

Ya ce Enang ya amsa masa da cewa:

“Idan ba ka ba ka ba ni abin yi ba, ba zan daina ba.”

Akpabio wanda yake jagorantar majalisa ya ce daga nan ne ya yanke shawarar tura Enang a matsayin jakadan Najeriya a Jamus.

“Saboda haka, na yanke shawarar tura shi matsayin jakada a Jamus. Ina so in yi maraba ta musamman da jakadan Najeriya a Jamus, Ambasada Ita Enang.”

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

- Godswill Akpabio

Cikin ba'a, tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya nuna cewa za su cigaba da bin wannan salo don ganin bayan 'yan adawar Eno.

Akpabio ya ƙara da cewa:

“Saboda haka, Gwamna Umo Eno, idan akwai wani mutum da yake damunka, ka ba ni aikin. Zan ba shi wani abu da zai yi, kuma ba zai sake yi maka magana ba.”

Akpabio ya gabatar da Enang a coci

A wani bidiyo da yake yawo a X, Akpabio ya gabatar da Enang a matsayin jakadan Najeriya a Jamus a tsakiyar cocin.

Daga nan ya yi wa tsohon hadimin shugaban kasar maraba a gaban mahalarta taron a Uyo.

Enang ya miƙe tsaye, yana murmushi tare da daga hannu ga mahalarta, lamarin da ya nuna amincewarsa da gabatarwar.

Kafin wannan kujera da ya samu, ya kasance Mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a a harkokin Majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya zabi manyan hadiminsa da gwamnoni 5, ya shirya masu liyafa a Makkah

Sheikh Jalo Jalingo ya ce a zabi APC

An samu labari Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo bai goyon bayan a zabi wata jam’iyyar da ba APC ba a takarar 2027 a Taraba.

Babban malamin na kungiyar Izala ya cigaba da tallar Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, yana ganin zaben su ne mafita.

Sheikh Jalo Jalingo ya ce an yi shekara da shekaru ana gallaza masu a siyasar jihar Taraba don haka kyau kawai su bi jirgin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng