Abubuwan da Tinubu Ya Fada kan Zabe bayan Shiga Dakin Ka'aba a Saudi
- Bayan shiga Ka'aba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa Najeriya hidima da kuma gina ƙasa mai wadata
- Tinubu ya bayyana cewa ya roƙi Allah Ya ba shi hikima da ƙarfin jure ƙalubale domin ci gaba da yi wa 'yan Najeriya hidima,
- Shugaban ƙasar ya kuma ce aniyar gwamnatinsa ta gina Najeriya da samar da makoma mai kyau ga matasa ta ƙara ƙarfi bayan wannan tafiya ta ibada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta gina Najeriya da samar da kyakkyawar makoma ga matasa, yana mai cewa zai ci gaba da gudanar da mulki bisa yardar Allah da muradin al'umma.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake tsokaci kan ziyarar ibadar Umara da ya kai ƙasar Saudiyya, inda Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya ba shi dama ta musamman ta shiga cikin Ka'aba.

Source: Facebook
Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Sheikh Dahlulah Muthawal na Masallacin Harami ne ya jagoranci shugaban ƙasar zuwa cikin Ka'aba, inda ya gudanar da addu'o'in godiya ga Allah bisa damar da ya ba shi ta zama shugaban Najeriya.
Tinubu ya gode wa Sarkin Saudiyya
Shugaba Tinubu ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa ba shi da tawagarsa damar shiga cikin Ka'aba da gudanar da addu'o'i.
Ya bayyana damar a matsayin wata babbar ni'ima da ba za ta gushe daga tarihinsa ba, wadda kuma ke nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya.
"Abin alfahari ne da na samu wannan dama, kuma abin karamci ne da suka ba mu damar shiga cikin Ka'aba."
Addu'ar da Tinubu ya yi a Ka'aba
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa daga cikin addu'o'in da ya yi a cikin Ka'aba akwai roƙon Allah Ya ƙara masa hikima da ƙarfin jure ƙalubale domin ci gaba da yi wa al'ummar Najeriya hidima.
Ya ce yana da yakinin cewa Allah Ya karɓi addu'arsa, yana mai cewa ya taɓa yin irin wannan addu'a kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
"Na roƙi Allah Ya ba ni hikima da ƙarfin jure ƙalubale domin ci gaba da yi wa al'umma hidima. Na san cewa an karɓi addu'ata. Kafin zaɓen 2023, na yi irin wannan addu'a lokacin da na gudanar da Umara, kuma Allah Ya amsa mini.
"Na yi alƙawarin cewa zan dawo domin gode masa."
Tinubu ya kuma yi tsokaci kan aya ta 26 a cikin Suratul Ali Imran, wadda ta bayyana cewa Allah ne mamallakin dukkan mulki, Yana ba wanda Ya so mulki, kuma Yana karɓe shi daga wanda Ya so.

Source: Facebook
Ya ce wannan aya tana tunatar da shugabanni cewa mulki amana ne da ya kamata su gudanar cikin tawali'u da adalci, domin Allah ne kaɗai ke ba da iko kuma Yana karɓe shi a duk lokacin da Ya so.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa imaninsa da Allah ya ƙara masa tabbacin cewa samun damar jagorantar Najeriya wata babbar ni'ima ce da ke buƙatar sadaukarwa wajen yi wa al'umma hidima.
APM ta caccaki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye takararsa ta neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.
Daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa na ƙungiyar, Richard Ihediwa, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake mayar da martani kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi zuwa ƙasashen waje.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa Tinubu ba shi da ƙarfin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da mulki, tana mai cewa Najeriya na buƙatar shugaban da zai iya jure ƙalubalen jagorancin ƙasa.
Asali: Legit.ng


