Shugaban kasa ba zai kara yin na’am da wani kudiri daga Majalisa ba – Ita Enang

Shugaban kasa ba zai kara yin na’am da wani kudiri daga Majalisa ba – Ita Enang

Labari ya zo mana cewa fadar shugaban kasa tace ba za ta sake sa hannu a kan duk wani kudiri da aka kawo mata a yanzu ba. Fadar shugaban kasar ta fitar da wannan jawabi ne a Ranar Lahadin nan.

Shugaban kasa ba zai kara yin na’am da wani kudiri daga Majalisa ba – Ita Enang

Shugaban kasa Buhari yace lokacin sa hannu a kudirorin garambawul ya kure
Source: Depositphotos

Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi cewa a halin yanzu lokaci ya kure da Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kan kudirorin da majalisa za ta aiko masa. Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne ta bakin Sanata Ita Enang.

Mai ma ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin majalisa, Ita Enang, yace idan har aka kawowa shugaban kasa wani kudiri a halin yanzu, ba zai rattaba hannu ba domin kuwa lokacin sa-hannu ya riga ya kure.

KU KARANTA: Ana kokarin yin ram da wasu ‘Yan Majalisa saboda yi wa Buhari ihu – PDP

Ita Enang yace kwanaki shugaba Buhari ya sa hannu a kan wasu kudirorin da aka aiko masa daga majalisa, sannan ya kuma maida wasu. Enang yace yanzu babu wani isasshen lokaci da za a rattaba hannu kan wani sabon kudiri.

Mai ba shugaban kasar shawara yace Buhari zai sanar da shugabannin majalisar wakilai da dattawa game da kurewar lokaci wajen yi wa tsarin mulkin kasa wani garambawul har sai an kafa wata sabuwar majalisa a wani gwamnati.

Majalisar tarayya ta aikowa shugaban kasa kudirori kusan 17 bayan sun yi kokarin yi wa tsarin mulkin kasar kwaskwarima sau 33. Shugaban kasar yayi fatali da wasu kudirorin da aka aiko masa, daga ciki har da kudirin zaben kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel