Siyasa ta Fara Sauya Salo: Gwamnatin Sokoto Ta Rufe Ofishin ADC

Siyasa ta Fara Sauya Salo: Gwamnatin Sokoto Ta Rufe Ofishin ADC

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe daya daga cikin ofisoshin jam’iyyar ADC bisa zargin cewa takaddamar mallakar ginin na iya haddasa matsalar tsaro
  • Kwamishinan filaye da gidaje, Nasiru Dantsoho, ya ce bincike ya nuna cewa ginin mallakin tsohuwar bankin Savannah ne, ba tare da canjin mallaka ba
  • Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da rike ginin har sai NDIC ta fayyace mai shi, tare da gargadin hukunta duk wanda ya kutsa cikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto – Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe daya daga cikin ofisoshin jam’iyyar ADC mai adawa sakamakon takaddamar mallakar ginin da ke cikinsa.

Kwamishinan filaye da gidaje na jihar, Barista Nasiru Dantsoho, ne ya sanar da rufe ginin a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026.

An rufe ofishin ADC a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Dantsoho ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyi, bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar da wasu bata-gari, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fallasa danyen aikin da Buhari ya yi da ya bar Tinubu da wahala

Zargin da ake yi kan ofishin ADC

Kwamishinan ya yi zargin cewa gwamnati ta gudanar da nazari kan takardun mallakar ginin, inda ta gano cewa tsohuwar bankin Savannah ce ta mallake shi.

Ya ce babu wata takardar hukuma da ta nuna an sauya mallakar ginin zuwa wani mutum ko hukuma tun bayan mallakar bankin.

Dantsoho ya bayyana cewa gwamnati ta rubuta wa Hukumar Inshorar Ajiya ta Najeriya (NDIC), wadda ya ce ita ce ke kula da kadarar, domin neman karin bayani kan mai mallakarta.

Sai dai ya ce har yanzu hukumar ba ta mayar da martani ga wasikar da gwamnati ta aika mata ba.

Da yake karin bayani, kwamishinan ya ce:

“Bayan nazarin takardar shaidar mallakar filaye da sauran muhimman takardu, mun gano cewa wannan kadarar mallakin bankin Savannah ce, kuma har zuwa yau ba a sauya mallakarta ba.
“Mun rubuta wa NDIC, wadda ke kula da wannan gini, domin ta fayyace mana wanda yake da mallakarsa a yanzu, amma har yanzu ba mu samu amsa ba.”

Kara karanta wannan

Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC

An rufe ofishin ADC a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto da ofishin ADC. Hoto: Ahmed Aliyu.
Source: Facebook

Musabbabin rufe ofishin ADC a Sokoto

Kwamishinan ya ce gwamnatin Sokoto ta yanke shawarar rufe ginin har sai NDIC ta mayar da martani kan tambayar da aka aika mata.

Ya jaddada cewa matakin ya zama dole domin hana sake samun rikici da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Dantsoho ya bukaci duk wanda yake ikirarin mallakar ginin da ya gabatar wa gwamnati da takardun da za su tabbatar da hakkin mallakarsa.

Ya ce bayan tantance takardun da kuma kammala dukkan matakan rajista, gwamnati za ta iya mika kadarar ga wanda ya mallake ta bisa ka'ida.

Sai dai kwamishinan ya jaddada cewa ginin zai ci gaba da kasancewa karkashin ikon gwamnatin jihar har sai an warware takaddamar mallakarsa.

Martanin Tambuwal game da hari kan ADC

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka ruwaito an kai wa dan takarar gwamnan ADC, Manir Muhammad Dan’iya, da tawagarsa.

Kara karanta wannan

Kebbi: Gwamnati ta yi maganar ‘rusa’ ginin tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami

Tambuwal ya bukaci rundunar ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike mai zaman kansa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu

Ya kuma yi kira ga magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa babu barazana da za ta hana jam’iyyar gudanar da gangami da kamfen a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.