2027: An Fadi Matsalolin da Suka Sa Atiku daga Ranar Kaddamar da Kamfen

2027: An Fadi Matsalolin da Suka Sa Atiku daga Ranar Kaddamar da Kamfen

  • Jam’iyyar ADC ta ɗage ƙaddamar da kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa a jihar Sokoto daga ranar Asabar, 31 ga Oktoba, zuwa Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026
  • Sauya ranar na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke zargin gwamnatin jihar Sokoto da hana otal-otal karɓar baƙin da za su halarci taron, zargin da gwamnatin ta musanta
  • Taron dai ana sa ran zai samu halartar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Aminu Tambuwal da sauran manyan shugabannin jam’iyyar, yayin da ake ƙara shirye-shiryen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sokoto – Jam’iyyar ADC ta ɗage bikin ƙaddamar da kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa a jihar Sokoto, wanda aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 31 ga Oktoba, zuwa Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.

Wani jigo a jam’iyyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana a bainar jama’a kan lamarin, ne ya tabbatar da sauyin ranar ga wakilin jaridar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Atiku Abubakar da manyan ADC
Jiga-jigan 'yan ADC a wajen taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce ba za a gudanar da taron ranar Asabar ba, amma ana buƙatar tabbatar da sabuwar ranar.

A cikin wata sanarwa da majalisar kamfen ɗin shugaban ƙasa ta ADC a jihar Sokoto ta fitar, ta danganta ɗage taron da buƙatar gyara wasu shirye-shirye da daidaita yadda za a gudanar da shi.

ADC ta sauya ranar kamfen

Majalisar kamfen ɗin ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da nasarar gudanar da taron.

Ta kuma nemi afuwar shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, magoya baya da sauran jama’a kan duk wata matsala da sauyin ranar zai iya haifarwa.

Sanarwar ta ce majalisar kamfen ɗin tana godiya ga masu goyon bayan jam’iyyar bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna, tare da kira ga mambobi da sauran masu ruwa da tsaki su lura da sabuwar ranar.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa tana shirye-shiryen tarbar shugabannin siyasa, magoya baya da sauran baƙin da za su halarci taron.

Kara karanta wannan

An tono yadda Sambo Dasuki ya raba biliyoyin kudin makamai zuw asusun bankuna

Zargin hana baƙin ADC masauki

Sauya ranar taron na zuwa ne yayin da ADC ke zargin gwamnatin jihar Sokoto da umartar otal-otal a babban birnin jihar da su hana baƙin da za su halarci ƙaddamar da kamfen ɗinta samun masauki.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa wasu baƙi da suka riga suka tanadi ɗakunan otal har suka shiga, an nemi su fice bayan wata doka da ake zargin an bayar.

Kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Dahiru Maishanu, ya ce wasu otal-otal sun sanar da mutanen da ke neman ɗakuna cewa duk sun cika har zuwa ranar Lahadi.

Maishanu ya bayyana hakan a matsayin yunƙurin hana jam’iyyar gudanar da harkokinta na siyasa da kuma hana magoya bayanta da za su zo daga sassa daban-daban na ƙasar halartar taron.

Tribune ta wallafa cewa ya ce:

“Wannan mataki yana nuna rashin da’a wajen amfani da ikon gwamnati da kuma nuna son kai a siyasa ba tare da dalili ba.”

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Ya kuma tambayi dalilin da zai sa gwamnati ta yi katsalandan cikin harkokin otal-otal masu zaman kansu, har ta hana mutanen da suka biya kuɗin ɗakuna samun masauki.

Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Gwamnatin Sokoto ta musanta zargin

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Sokoto, Sambo Danchadi, ya musanta zargin cewa gwamnati ta bayar da umarnin hana otal-otal karɓar baƙin ADC.

Da yake magana ta wayar tarho, Danchadi ya bayyana zargin a matsayin jita-jitar da ba ta da hujja, yana mai cewa gwamnati ba ta da niyyar tsoma baki cikin harkokin kasuwancin otal-otal.

NDC na son hadaka da ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa jigon NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya buƙaci shugabannin hamayya, ciki har da Atiku Abubakar, su haɗa kai da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Abdulkarim ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce haɗakar hamayyar ta riga ta fara, tare da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da Kwankwaso ya amince ya yi aiki tare da shi.

Ya bayyana cewa ba lallai ne haɗakar ta kasance ƙarƙashin ADC ba, domin za a iya gina ta a ƙarƙashin NDC. Ya ce manufar ita ce a haɗa ƙarfin ’yan adawa a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng