INEC Ta Saka Ranar Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a Najeriya

INEC Ta Saka Ranar Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a Najeriya

  • Hukumar INEC ta sanya ranar 28 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri’a a faɗin Najeriya
  • Gwajin zai taimaka wajn tantance ingancin na’urar BVAS da tsarin aika sakamakon zaɓe ta hanyar intanet kafin babban zaɓen 2027
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ta kuma fara raba wasu kayayyakin zaɓe ga wasu jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da shirinta na gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri’a a dukkan jihohin Najeriya a ranar 28 ga Nuwamba, 2026.

Hukumar ta ce gwajin wani shiri ne na tabbatar da ingancin na'urorin tantance masu zaɓe da tsarin aika sakamakon zaɓe ta hanyar intanet kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya gamu da matsala a ƙasar waje, mutane sun kewaye motarsa

Shugaban hukumar INEC a Najeriya
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa a cibiyar Chatham House da ke Landan.

Abin da gwajin INEC zai ƙunsa

A cewar Amupitan, gwajin zai kwaikwayi zaɓen shugaban ƙasa domin hukumar ta tabbatar da cewa tsarin tantance masu zaɓe da aika sakamakon zaɓe na aiki yadda ya kamata.

Ya ce:

“A ranar 28 ga wannan wata, za mu gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da kaɗa ƙuri’a a dukkan jihohin tarayya domin gwada zaɓen shugaban ƙasa da tabbatar da cewa mun samu nasarar tantance masu zaɓe da aika sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki.”

Shugaban INEC ya bayyana cewa gwajin zai ba hukumar damar gano duk wata matsala da ka iya tasowa kafin babban zaɓen 2027.

Wajen zaben jihar Osun
Masu kirga kuri'a a zaben Osun na 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Matakan kare sakamakon zaɓe

Amupitan ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙara samar da wasu matakan kariya na fasaha domin hana shigar da sakamakon zaɓen da ba daidai ba a shafinta na nuna sakamako.

Kara karanta wannan

IReV: INEC ta ɗauki darasi, ta magance abin da ake tsoron zai iya faruwa a zaben 2027

Ya ce matakan za su hana loda sakamakon rumfunan zaɓe da ke ɗauke da alkaluman da ba su dace ba, musamman waɗanda suka nuna an kaɗa ƙuri'a fiye da yawan masu zaɓe da aka tantance.

A wani mataki na shirye-shiryen zaɓen 2027, shugaban INEC ya ce hukumar ta fara raba kayayyakin zaɓe marasa muhimmanci ga wasu jihohin ƙasar.

A wani ɓangaren taron na Chatham House, shugaban INEC ya musanta mallakar wani shafin sada zumunta na X da ake zargin an yi amfani da shi wajen nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Magana kan takarar Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar za ta bi duk hukuncin da kotu ta yanke kan yiwuwar Atiku Abubakar ya tsaya takara.

Amupitan ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya wajabta wa INEC bin umarnin kotuna, musamman Kotun Ƙoli, ba tare da la'akari da ra'ayin jama'a kan hukuncin ba.

Ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa a Chatham House da ke Landan, inda aka tambaye shi ko Atiku zai iya tsayawa takara a ƙarƙashin ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng