"Ba Cin Mutunci Kowa," Gwamna Ya Ce Suna da Abin da Za Su Tallata APC wurin Yan Najeriya a 2027
- Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙalubalanci jam’iyyun adawa su bayyan
- a ayyukan da suka gudanar lokacin da suke kan mulki gabanin zaɓen 2027
- Ya ce jam’iyyar APC za ta yi kamfen ne bisa ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta gudanar, ba tare da cin mutuncin abokan hamayya ba
- Gwamnan ya buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu su mutunta ra’ayoyin juna, su kuma guji amfani da ’yancin faɗar albarkacin baki wajen tauye haƙƙin wasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙalubalanci jam’iyyun adawa a jihar da su gabatar wa talakawa da nasarorin da suka samu a lokacin da suke kan mulki.
Gwamna Ahmed Aliyu ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tallata kanta a wurin mutanen Sakkwato ne bisa ayyuka da shirye-shiryen raya ƙasa da ta aiwatar.

Source: Facebook
A rahoton Vanguard, Aliyu ya ce jam’iyyar APC za ta mayar da hankali kan ayyukan da ta gudanar tun bayan hawanta mulki, maimakon shiga musayar yawu ko yaƙin ɓata sunan abokan hamayyar siyasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar gwamnati da ke Sakkwato ranar Juma’a, jim kaɗan bayan halartar sallar Juma’a.
Gwamna Aliyu ya ja hankalin yan adawa
Ya yi kira da a gudanar da kamfe bisa batutuwan da suka shafi al’umma da kuma ɗabi’ar siyasa mai kyau gabanin zaɓen 2027 da ke kara gabatowa.
“Za mu tabbatar da cewa muna amfani da kalaman mutunci lokacin mamfe kuma za mu guji cin zarafin kowa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya kamata gasar siyasa ta mayar da hankali kan nasarorin da aka samu, manufofin da za a iya aiwatarwa da kuma tattaunawa mai amfani.
Yadda APC za ta yi kamfe a Sakkwato
Gwamna Aliyu ya dage cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka da dama a sassa daban-daban na jihar, yana mai cewa waɗannan ayyuka za su zama ginshiƙin kamfen ɗin APC domin samun wa’adin mulki na gaba.

Kara karanta wannan
To fa: Gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan sababbin hanyoyin da 'yan ta'adda suka bullo da su
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da sauraron koke-koken mazauna jihar da kuma ɗaukar matakan biyan buƙatunsu, yana mai jaddada cewa ya kamata a yi amfani da mukaman gwamnati wajen inganta rayuwar jama’a da bunƙasa jihar.

Source: Facebook
Gwamna Aliyu ya kalubalanci yan adawa
Da yake ƙalubalantar jam’iyyun adawa da su bayyana abin da suka cimma a lokacin mulkinsu, gwamnan ya buƙaci yan adawa su tallata kansu xa nasarorinsu da manufofinsu maimakon sukar gwamnatin da ke kan mulki.
“Maimakon komawa ga yaƙin ɓata suna, ya kamata jam’iyyun adawa su gaya wa jama’a abin da suka cimma lokacin da suke kan mulki,” in ji shi.
Aliyu ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan amfani da ’yancin faɗar albarkacin baki ta hanyar da za ta cutar da wasu yayin kamfen.
Ya ce bai kamata a yi amfani da haƙƙoƙin dimokuraɗiyya wajen tauye haƙƙin wasu, cin mutuncinsu ko barazana tsaron rayukansu ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Aliyu zai magance matsalar tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Sokoto ta ce ta ayyana yaƙi da ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka bayan wani mummunan hari da ya kashe mutane a Kebbe.
Gwamnatin ta ce Gwamna Ahmed Aliyu ya ƙuduri aniyar ƙara ƙarfafa matakan da jihar ke ɗauka domin magance matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng
