Tinubu Ya Kira Ruwa, Dino Melaye Ya Yi Masa Tatas kan Zaben 2027
- Dino Melaye ya ce Shugaba Bola Tinubu bai cancanci sake samun wa’adi ba, bisa zargin cewa gwamnatinsa ta ƙara tsananta yunwa da talauci
- Sanatan ya bukaci al’ummar Bauchi da sauran ’yan Najeriya su mara wa Atiku Abubakar na ADC baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ɗan takarar gwamnan Bauchi na ADC, Sanata Halliru Dauda Jika, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar su kare ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Sanata Dino Melaye, jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jefa ’yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa da wahalhalun tattalin arziki.
Melaye ya bayyana cewa Tinubu bai cancanci sake samun wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa ba, inda ya bukaci ’yan Najeriya su kaɗa ƙuri’unsu domin sauya gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Malamin addini ya hango ministan da zai kawo cikas ta tazarcen Tinubu

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Dino Melaye ya bukaci a zaɓi Atiku a 2027
Sanatan ya yi zargin cewa APC da gwamnatin Tinubu ba su da ingantaccen shiri na magance matsalolin tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta, musamman yunwa da talauci.
Ya yi kira ga mazauna jihar Bauchi, al’ummar Arewa da sauran ’yan Najeriya da su mara wa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, baya domin ya maye gurbin Tinubu a 2027.
A cewarsa, APC ta rasa tasirinta a siyasar Najeriya, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin ADC ƙarƙashin Atiku za ta magance yunwa, talauci da sauran matsalolin da ke addabar ƙasar.
Melaye ya jaddada cewa ’yan Najeriya sun cancanci samun gwamnatin da za ta iya magance matsalolin tattalin arzikinsu da inganta rayuwarsu.
An yi kira kan kare ƙuri’u
A jawabin maraba da baƙi, ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na ADC, Sanata Halliru Dauda Jika, ya bayyana cewa jam’iyyar na da kyakkyawan shiri da damar lashe zaɓen 2027.
Jika ya danganta hakan da tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa da kuma yawan magoya bayanta a sassa daban-daban na Najeriya.
Ya jaddada cewa nasarar zaɓe tana farawa ne daga rumfunan zaɓe, saboda haka ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya.
Ya kuma bukace su da su kaɗa ƙuri’unsu, su zauna a rumfunan zaɓe domin kare ƙuri’unsu, tare da tabbatar da cewa an bayyana sakamakon zaɓe yadda ya kamata a matakin rumfa.
ADC ta gargaɗi magoya bayanta
Jika ya ce:
"Ana lashe zaɓe ne a matakin rumfunan zaɓe. Saboda haka, ina kira gare ku da ku fito, ku kaɗa ƙuri’unku, ku zauna a rumfunan zaɓe, ku kare ƙuri’unku, sannan ku tabbatar an bayyana sakamakon yadda ya kamata a matakin rumfa.”
Ya kuma gargaɗi magoya bayan jam’iyyar da kada su bari wani ya yi amfani da su wajen sauya ko yin katsalandan a tsarin zaɓe.
Ya ƙara da cewa:
“Dole ne mu kasance cikin shiri da sanya ido, domin tabbatar da cewa babu wanda ya yi wa muradin jama’a da suka bayyana ta hanyar ƙuri’unsu katsalandan.”

Source: Facebook
Masu goyon bayan Tinubu sun koma wajen Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna Tinubu Northern Youth Forum ta sanar da janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar baya.
Kungiyar ta sanar da sauya sunanta zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), a matsayin wani ɓangare na sabon matsayinta na siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

