Halin da Dalibai Sama da 150 ke Ciki bayan Sun Sha Wani Magani da Ya Masu Illa a Katsina

Halin da Dalibai Sama da 150 ke Ciki bayan Sun Sha Wani Magani da Ya Masu Illa a Katsina

  • ’Yan sandan Katsina sun tabbatar da cewa an sallami dukkan ɗalibai 154 da suka kamu da rashin lafiya bayan shan maganin cutar Bilharzia daga asibiti
  • Ba a samu rahoton mutuwar ko ɗalibi ɗaya ba, amma har yanzu ba a bayyana ainihin abin da ya haddasa matsalar ba
  • Daliban sun fara nuna alamomin amai, ciwon ciki da jiri bayan shan maganin Praziquantel ranar 26 ga Oktoba, 2026 a Batagarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Dukkan ɗalibai 154 da suka kamu da rashin lafiya bayan shan magani a makarantar sakandare ta kwan da ke Batagarawa, jihar Katsina, sun warke kuma an sallame su daga asibiti, a cewar ’yan sanda.

Ba a samu rahoton mutuwar ko ɗalibi ɗaya ba, sai dai har yanzu ba a bayyana wa jama’a ainihin abin da ya haddasa lamarin ba.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta ce ɗaliban sun fara nuna alamomin rashin lafiya ne bayan an ba su ƙwayoyin maganin Praziquantel a wani shirin yaƙi da cutar Bilharzia ranar Litinin, 26 ga Oktoba.

Halin da daliban Batagarawa ke ciki

A cikin wata sanarwa mai kwanan wata Laraba, 28 ga Oktoba, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, Abubakar Aliyu, ya ce sauran ɗalibai 25 da ke karɓar kulawar likitoci sun warke kuma an sallame su.

“Domin kawar da duk wani shakku, dukkan ɗalibai 154 da suka nuna alamomin illa bayan an ba su ƙwayoyin maganin Praziquantel, waɗanda daga baya aka kai su asibitoci, yanzu an sallame su bayan sun warke sarai,” in ji Aliyu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Fage, ya gode wa mazauna jihar bisa haɗin kai da suka bayar, tare da kira gare su da su yi watsi da rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba game da lamarin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Sanarwar ta biyo bayan bayanin da gwamnatin jihar Katsina ta fitar a baya cewa ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Abin da ya faru a makarantar

Hukumomin kula da lafiya a matakin farko ne suka gudanar da shirin bayar da maganin tare da haɗin gwiwar ƙaramar hukumar Batagarawa.

A cewar jaridar The Sun, an ba ɗalibai sama da 700 maganin a rukuni biyu. An gudanar da kashi na farko na shirin ranar 24 ga Oktoba, ba tare da samun wata matsala ba.

Sai dai a kashi na biyu da aka gudanar ranar 26 ga Oktoba, 2026 wasu ɗalibai sun fara nuna alamomin rashin lafiya, ciki har da amai, ciwon ciki da jiri.

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a fadar gwamnatinsa Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Source: Facebook

An kai wasu daga cikinsu asibitin Ahmadi Rimi Specialist Hospital da kuma Turai Yar’Adua Maternal and Child Hospital da ke Katsina.

A halin yanzu rundunar yan ssnda ta tabbatar da cewa duka daliban sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

Yan sanda sun kama mutane 14

Kun ji cewa ’yan sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da kai hari kan ayarin magoya bayan APC a hanyar Yashe zuwa Funtua da ke jihar Katsina.

Rundunar yan sanda ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan aikata abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262