An Fara Gano Kura Kurai a Shirin Zaben 2027, Kwankwaso Ya Gargaɗi INEC
- Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi INEC kan zargin amfani da hotunan bogi da aka samar da fasahar AI a rajistar masu zaɓe
- Tsohon gwamnan Kano ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya kan rajistar, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi
- Kwankwaso ya ce dole ne INEC ta tabbatar da ingancin rajistar masu zaɓe, domin kare dimokuraɗiyyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tura sakon gargadi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Kwankwaso ya ce samun kura-kurai a rajistar masu zaɓe ta farko na iya kawo cikas ga sahihancin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027
Kwankwaso ya gargadi hukumar INEC
Hakan ya biyo bayan rahotannin zargin samun hotunan da aka samar ta amfani da fasahar basirar ɗan’adam (AI) da wasu bayanai masu tayar da hankali a rajistar.
Ya yi gargaɗin cewa rashin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen na iya rage amincewar jama’a ga tsarin zaɓen Najeriya gabanin babban zaɓen da ke tafe.
A cewarsa, wannan lamari ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan ingancin tsarin rajistar masu zaɓe da matakan da INEC ta ɗauka domin hana maguɗin zaɓe.
Ya ce:
“Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, dole ne INEC ta bai wa ’yan Najeriya amsoshi bayyanannu kuma masu gamsarwa."

Source: Twitter
Kwankwaso ya ƙalubalanci hukumar INEC
Kwankwaso ya ƙalubalanci yadda hotunan da ake zargi suka shiga rajistar, ko mutanen da abin ya shafa sun yi rajista da gaske, da kuma ko an tantance sahihancin bayanan da ke tabbatar da asalinsu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki
Duk da maraba da matakin INEC na gudanar da bincike kan zarge-zargen, tsohon gwamnan ya jaddada cewa ’yan Najeriya sun cancanci samun fiye da tabbaci kawai daga hukumar zaɓen.
Ya bukaci gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da zaman kansa, yana mai cewa dole ne a bayyana sakamakon binciken ga jama’a, sannan a hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.
Shawarar Kwankwaso ga Hukumar zabe
Haka kuma, Kwankwaso ya bukaci gudanar da cikakken binciken rajistar masu zaɓe ta farko karkashin wani kwamiti mai zaman kansa, domin gano bayanan da ake zargi, rajista fiye da ɗaya da kuma yiwuwar amfani da sunayen mutanen da ba su wanzu.
Sai dai ya jaddada cewa wannan aikin bai kamata ya hana ’yan Najeriya da suka cancanci yin zaɓe amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki ba.
“Dimokuraɗiyyarmu ba za ta iya jure duk wani abu da zai lalata ingancin rajistar masu zaɓe ba. Dole ne kowane ɗan Najeriya da ya cancanta ya samu damar yin zaɓe, kuma kowace ƙuri’a ta ƙidayu.
“Bai kamata a bar kowa ya yi amfani da fasaha, ciki har da basirar ɗan’adam, wajen lalata tsarin zaɓenmu ba."
- In ji Kwankwaso.
Tsohon gwamnan ya kuma yi gargaɗi kan amfani da sabbin fasahohi, musamman basirar ɗan’adam (AI), wajen yin maguɗi a tsarin zaɓe.
Peter Obi ya yi barazana ga jami'an INEC
A baya, an ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi barazanar hukunta duk wanda ya yi magudin zaɓe.
Obi ya ce jami’an INEC da duk masu hannu a gudanar da zaɓe da aka samu da laifin maguɗi za su fuskanci ɗaurin kurkuku.
Tsohon gwamnan Anambra ya kuma buƙaci tsaurara dokokin cancantar tsayawa takara.
Asali: Legit.ng
