Atiku v Amaechi: Wike Ya Lissafo Matsaloli 2 da Ke Tattare da Tikitin ADC
- Wike ya buƙaci Atiku Abubakar ya bayyana irin nasarorin da ya samu a shekaru takwas da ya yi mataimakin shugaban ƙasa
- Ministan ya ce shigar Rotimi Amaechi cikin ADC ta ƙara rikitar da fafatawar neman tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar
- Wike ya nemi a yi bayani kan kuɗaɗen wasu ayyukan da ake dangantawa da gwamnatin Amaechi a Rivers, ciki har da aikin layin dogo na cikin birni da aka ce ya lakume Naira biliyan 68
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kalubalanci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya bayyana irin nasarorin da ya samu a shekaru takwas da ya yi a kan mulki.
Wike ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su yi la’akari da sukar da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi wa tsohon mataimakinsa, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2026 wani taron Rainbow Coalition da aka gudanar a ƙaramar hukumar Oyigbo ta Jihar Rivers, cewar rahoton jaridar Leadership.
Wike ya jero tambayoyi ga Atiku
Wike ya ce Atiku ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, kuma yana da babban iko a gwamnatin tarayya, musamman wajen kula da shirin sayar da kadarorin gwamnati.
A cewar Wike, Atiku ba mataimakin shugaban ƙasa ne kawai ba, domin yana da alhakin kula da batutuwan da suka shafi kamfanoni da masana’antun gwamnati.
Ministan ya bayyana cewa shi ma ya taɓa fafatawa da Atiku a zaɓen fitar da gwani na takarar shugaban ƙasa, inda ya buƙaci jama’a su mayar da hankali kan ayyukan tsohon mataimakin shugaban ƙasar maimakon yawan yunƙurinsa na neman shugabancin Najeriya.
Wike ya tambayi masu sauraro ko za su iya nuna irin tasirin da Atiku ya yi a lokacin da yake kan mulki, yana mai cewa ya kamata a tantance aikinsa kafin a sake ba shi damar neman shugabancin ƙasar.
Ya kawo daganar sukar Obasanjo kan Atiku
Wike ya kuma yi tsokaci kan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda ya taɓa sukar Atiku, ciki har da rahotannin da suka nuna cewa ya yi nadamar goyon bayan zaɓen tsohon mataimakinsa a wannan matsayi.
Ministan ya ce ya kamata a yi la’akari da yadda dangantakar siyasar Obasanjo da Atiku ta kasance wajen tantance tarihin tsohon mataimakin shugaban ƙasar, yayin da yake neman shugabancin Najeriya a karo na gaba.
Wike Ya kalubalanci ADC tikin Atiku, Amaechi
Ministan ya kuma nuna shakku kan ikon jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na samar da ingantaccen madadin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ya ce shigar tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, cikin jam’iyyar ta ƙara rikitar da fafatawar neman tikitin takarar shugaban ƙasa.
Wike ya buƙaci masu ruwa da tsaki a siyasa su binciki tarihin Atiku da Amaechi, musamman ayyukan da aka gudanar da kuɗaɗen da aka kashe a lokacin da Amaechi ya kasance gwamnan Rivers daga 2007 zuwa 2015.

Kara karanta wannan
"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

Source: Facebook
Wike ya soki Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya ce bai kamata a zaɓi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin shugaban kasa ba.
Ministan na Abuja ya ce ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Chibuike Amaechi, bai cancanci rike kowane muƙami a ƙasar ba saboda zargin rashin kyakkyawan kula da kuɗaɗen gwamnati.
Asali: Legit.ng

