Akwai Babban dalili: Makiyaya Sun Faɗi Musabbabin Shirin Goyon bayan Tinubu

Akwai Babban dalili: Makiyaya Sun Faɗi Musabbabin Shirin Goyon bayan Tinubu

  • Kungiyoyin makiyaya a Najeriya sun gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo, tare da yi masa alƙawari
  • Ministan Raya Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana kafa ma’aikatar a shekarar 2024 a matsayin babban ci gaba
  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, da shugabannin kungiyoyin makiyaya sun yabawa Tinubu, tare da bayyana shirin goyon bayansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyoyin makiyaya daga sassa daban-daban na Najeriya sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Tinubu bisa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya.

Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Fulani makiyaya sun nuna goyon baya ga Tinubu
Dandazon makiyaya da suka nuna goyon baya ga Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Dalilin makiyaya na goyon bayan Tinubu

Haka kuma, sun ce sauye-sauyen za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Ba dalilin zaɓenka ba kenan': Ƴan Najeriya sun fusata da Tinubu ya je Makka addu'a

Kungiyoyi daban-daban na makiyaya ne suka haɗa kai wajen shirya taron, wanda ya samu halartar wakilan gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki.

Daga cikin mahalarta taron akwai manoman dabbobi, masu kiwon shanu, masu sarrafa kayayyakin kiwo, ’yan kasuwa da ƙungiyoyin manoma.

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Raya Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana kafa ma’aikatar a watan Yulin 2024 a matsayin wani babban ci gaba.

Ya ce kafa ma’aikatar ya kawo kulawa ta musamman ga harkar kiwo a matakin gwamnatin tarayya, bayan shekaru masu yawa ana neman hakan.

Maiha ya ce:

“Manoman dabbobi, makiyaya, masu kiwon shanu, manoman madara, ’yan kasuwar dabbobi, dillalai, masu safarar dabbobi, mahauta da masu sarrafa nama, wannan ma’aikatarku ce.
“Ku karɓe ta, ku mallake ta, sannan ku yi amfani da ita wajen inganta rayuwarku, samar da zaman lafiya, jituwa da wadata ga kowa.”
Uba Sani ya yaba gwamnatin Tinubu
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Facebook

Kalaman Gwamna Uba Sani na Kaduna

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda Kwamishinan Noma da Gandun Daji, Murtala Mohammed Dabo, ya wakilta, ya yaba wa Tinubu bisa kafa ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Atiku ya zargi Tinubu da shirin tafiya Faransa amma ya fake da zuwa Saudi

Gwamnan ya kuma jinjinawa Ministan Raya Kiwo bisa ƙoƙarinsa na aiwatar da sauye-sauye domin bunƙasa harkar kiwo a Najeriya, cewar Punch.

Uba Sani ya bayyana wasu shirye-shiryen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin taimaka wa makiyaya da sauran masu harkar dabbobi a Kaduna.

Abin da shugaban makiyaya ya ce

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙasa na Ƙungiyar Makiyayan Shanu ta Najeriya (MACBAN), Baba Othman Ngelzarma, ya bayyana kafa ma’aikatar a matsayin cikar burin makiyaya.

Ya ce al’ummar makiyaya sun kwashe shekaru da dama suna neman gwamnatin tarayya ta kafa ma’aikata ta musamman domin kula da harkokin kiwo.

Ngelzarma ya bayyana cewa an yi watsi da harkar kiwo tsawon shekaru, lamarin da ya taimaka wajen ƙara rikicin manoma da makiyaya.

Ya ce:

“An kafa ma’aikatar ne musamman domin magance matsalar samar da zaman lafiya, kuma abin da Ministan yake yi kenan.
“Zaman lafiya shi ne burinmu, ba mu kaɗai abin ya shafa ba, har da mu makiyaya.”

Amurka ta ji dadin kashe shugaban Fulani

Mun ba ku labarin cewa dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yaba da rahoton kama Mahmoud Adam da ke jihar Plateau.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

Moore ya ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na haifar da sakamako mai kyau, tare da yabawa gwamnatin Bola Tinubu.

An kawo rahoto cewa an kama Adam a gidansa da ke Plateau tun ranar 12 ga Satumbar 2026 da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.