Alfarmar da Shugabannin Arewa Suka Nema daga Tinubu saboda Zaɓen Buhari

Alfarmar da Shugabannin Arewa Suka Nema daga Tinubu saboda Zaɓen Buhari

  • Wani jigon APC, Magaji Da’u Aliyu, ya ce shugabannin Arewa sun roki Tinubu ya mara wa Buhari baya a zaben 2015
  • Aliyu ya ce an yi yarjejeniyar cewa bayan Buhari ya shafe shekaru takwas, za a mayar da mulki bangaren Tinubu
  • Ya bukaci al’ummar Arewa su mara wa Tinubu baya a 2027, yana mai cewa wajibi ne su cika alkawarin da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani tsohon dan majalisar wakilai a Jigawa ya tuna alfarmar da Arewa ta nema daga Bola Tinubu.

Injiniya Magaji Da’u Aliyu, ya yi ikirarin cewa shugabannin siyasar Arewa sun roki Bola Tinubu ya goyi bayan burin Muhammadu Buhari na zama shugaban kasa.

Taimakon da Tinubu ya yi wa Buhari
Marigayi Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Rahoton Vanguard ya ce dan siyasar ya ce sun yi alkawarin mayar da mulki bangarensa bayan shekaru takwas.

Kara karanta wannan

‘Dan majalisar Kano ya tuno alherin da Tinubu ya yi wa Buhari a kokarin tallar APC

'Dole Arewa ta goyi bayan Tinubu'

Aliyu, wanda kuma shi ne mataimakin daraktan yakin neman zaben kungiyar North for Tinubu Support Group, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Birnin Kudu.

Ya ce babu wani dalili da zai sa Arewa ta ki goyon bayan sake zaben Bola Tinubu a babban zaben 2027, yana mai jaddada cewa dole yankin ya cika yarjejeniyar siyasar da aka kulla kafin Buhari ya zama shugaban kasa a 2015.

A cewarsa, Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa sau uku ba tare da samun nasara ba, kafin shugabannin siyasar Arewa su tuntubi Tinubu a Legas domin neman goyon bayansa.

Aliyu ya ce:

“Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa sau uku amma ya sha kaye. Daga nan muka je Legas muka roki Tinubu ya goyi bayan burin Buhari na zama shugaban kasa.
“Ya amince zai taimaka mana bisa sharadin cewa bayan Buhari ya shafe shekaru takwas a mulki, za a mayar da mulki bangarensa, kuma muka amince da yarjejeniyar.”

Kara karanta wannan

'Dan ƙungiyar A4A, Aliyu Jalal ya ce gwamnatin Tinubu ta kusa dawo da tsaro a Najeriya

An tuna alherin Tinubu ga Buhari
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Ana son cika wa Tinubu alƙawari

Aliyu ya dage cewa goyon bayan sake zaben Tinubu a 2027 hanya ce ta cika alkawarin da aka dauka masa, yana mai cewa babu dalilin da zai sa mutanen Arewa su yi watsi da yarjejeniyar.

Ya ce:

“Ga duk wani dan Arewa, cika wannan yarjejeniya wajibi ne. Ba mu da wani dalilin kin cika alkawarin da muka dauka.”

Jigon na APC ya yi alkawarin cewa mambobin kungiyar Northern Tinubu Support Group za su sadaukar da dukiyoyinsu domin ganin Shugaba Tinubu ya yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Ya kara da cewa:

“A bangarenmu, za mu tallafa wa Tinubu ya sake lashe zabe da rayukanmu da dukiyoyinmu domin tabbatar da cika alkawarin da muka dauka.”

Magaji Da’u ya yi magana kan matsalar tsaro

Da yake magana kan matsalar tsaro, Aliyu ya kuma kare Shugaba Tinubu daga sukar da ake yi masa kan kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

APC ta koma ba Atiku shawara kan abin da ya kamata ya yi wa Tinubu a zaben 2027

Ya yi ikirarin cewa babu wani dan Adam da yake da cikakken ikon tabbatar da tsaro, yana mai cewa Allah ne kadai zai iya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dindindin.

Ya ce:

“Mu daina zargin juna. Allah kadai ne yake da ikon samar da tsaro. Ya kamata mu nemi gafararsa, kuma zai ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Alherin da Tinubu ya yi wa Buhari

Mun ba ku labarin cewa Abubakar Kabir Bichi ya ce Muhammadu Buhari ya lashe zaɓen 2015 ne saboda goyon bayan Bola Tinubu.

Saboda haka ya buƙaci ’yan Arewa su rama wannan alheri ta hanyar zaɓen shugaban Najeriyan a takarar 2027.

Hon. Bichi ya ce manyan APC a Kano ta Arewa sun sa burin samun ƙuri’u miliyan ɗaya a zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.