'Ba Mu Goyon bayan Kowace Jam'iyya a 2027,' Shugaban INEC

'Ba Mu Goyon bayan Kowace Jam'iyya a 2027,' Shugaban INEC

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da ɗan takarar da take so ko wata jam’iyyar siyasa da ta fi so a zaɓen 2027
  • Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce INEC za ta yi aiki bisa doka da kuma muradin masu zaɓe a Najeriya
  • Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta kammala matakai tara cikin 14 na shirye-shiryen zaɓen 2027, yayin da rajistar masu zaɓe ta ƙaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da ɗan takarar da take so ko jam’iyyar siyasa da ta fi so a babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi tawagar ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da ta zo duba shirye-shiryen zaɓe a Abuja.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC a ofis. Hoto: INec Nigeria
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Saliyo, Victor Bockarie Foh, ne ya jagoranci tawagar.

Amupitan ya ce hukumar na gudanar da rangadin tantance shirye-shiryen zaɓe a yankunan siyasa daban-daban na ƙasar domin shirin babban zaɓen 2027.

Matsayar INec kan zaɓen 2027

Amupitan ya jaddada cewa hukumar ba ta da wani ɗan takara ko jam’iyyar da take goyon baya a zaɓen mai zuwa.

Ya ce:

“INEC a ƙarƙashin jagorancina ba ta da ɗan takara ko wata jam’iyyar siyasa da take so.
“Abin da muke biyayya gare shi shi ne bin doka, ikon ’yan Najeriya na zaɓen shugabanninsu da kuma ci gaban dimokuraɗiyyar ƙasarmu.”

Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne a yankunan rajista 8,809 da ƙananan hukumomi 774 na Najeriya.

Bayani kan rajistar masu zaɓe

Rahotanni sun nuna cew Farfesa Amupitan ya bayyana cewa adadin masu zaɓe da ke rajistar Najeriya ya haura miliyan 103.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: INEC ta fara fargaba kan zaben 2027

Leadership ta rahoto ya ce hukumar ta kammala matakai tara cikin 14 da doka ta tanada a sabon jadawalin shirye-shiryen zaɓen da ta fitar.

A cewarsa, INEC ta kuma kammala matakai uku na ci gaba da rajistar masu zaɓe, tare da baje kolin rajistar farko ta masu zaɓe a faɗin ƙasar domin jama’a su duba bayanansu.

Wajen zaben Anambra
Yadda aka kada kuri'a a wajen zabe a Anambra. Hoto: INec Nigeria
Source: Facebook

Da yake magana a madadin tawagar ECOWAS, Victor Bockarie Foh ya ce ziyarar na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na tantance shirye-shiryen zaɓe a ƙasashen yankin da ke shirin gudanar da babban zaɓe.

Obi zai yi aiki da Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya sake bayyana shirinsa na yin aiki tare da Sanata Rabiu Kwankwaso, domin ciyar da Najeriya gaba.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da jama’a a Enugu, inda ya yi magana kan matsalolin ƙasar da kuma burin shi na ci gaban Najeriya.

Ya ce tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma zai kasance cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko, tare da magance matsalolin tsaron da ke barazana ga al’ummomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng