Ana Wata ga Wata: INEC Ta Fara Fargaba kan Zaben 2027

Ana Wata ga Wata: INEC Ta Fara Fargaba kan Zaben 2027

  • ​Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi gargaɗin cewa rashin tsaro na iya hana gudanar da zaɓen 2027 a wasu yankunan Najeriya
  • Amupitan ya ce zai gana da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa da sauran jami’an tsaro domin tattauna matakan shawo kan matsalar
  • INEC ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da ’yan sanda, NSCDC, DSS da sojoji domin inganta tsaro da shirye-shiryen gudanar da zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta nuna damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro za ta iya kawo cikas ga gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, ko ma hana gudanar da shi a wasu sassan ƙasar.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2026 a Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin sanya INEC dage zaben 2027? An ji yadda zancen yake

INEC ta fara fargaba kan zaben 2027
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mahalarta taron shiyya na Arewa maso Gabas da aka gudanar domin duba shirye-shiryen ma’aikatan INEC da kuma tantance shirinta na zaɓen 2027.

Amupitan zai gana da manyan jami’an tsaro

Amupitan ya bayyana rashin tsaro a wasu sassan Najeriya a matsayin babban ƙalubale ga gudanar da sahihin zaɓe, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa da haɗin kai domin kare harkokin zaɓe.

Ya ce bayan komawarsa Abuja, zai gana da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa da sauran manyan jami’an tsaro domin tattauna hanyoyin magance barazanar tsaro da samar da yanayin da ya dace da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Shugaban INEC ya jaddada cewa hukumar za ta riƙa ɗaukar matakan kariya tun da wuri, maimakon jiran barazanar tsaro ta tsananta kafin ta fara ɗaukar mataki.

Kara karanta wannan

Ana batun shirin dage zaben 2027, majalisa ta gayyaci shugaban INEC

INEC ta karfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro

Amupitan ya bayyana cewa INEC na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da rundunar ’yan sandan Najeriya, Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), Hukumar DSS, rundunonin sojoji da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Ya ce ana gudanar da wannan aiki ne ta hanyar Kwamitin Haɗin Gwiwa tsakanin Hukumomin da ke da alhakin Tsaron Zaɓe (ICCES), domin inganta musayar bayanan sirri, daidaita ayyukan tsaro da kuma ƙara shirin ko-ta-kwana gabanin zaɓen 2027.

A cewarsa, wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen tabbatar da cewa hukumomin da abin ya shafa sun shirya tinkarar matsalolin tsaro da ka iya tasowa yayin gudanar da zaɓe.

Yadda rashin tsaro zai iya shafar zaɓen 2027

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ke ƙara shirye-shiryen babban zaɓen 2027, yayin da rashin tsaro ke zama barazana ga gudanar da muhimman ayyukan zaɓe a yankunan da abin ya shafa.

Matsalar na iya hana ma’aikatan zaɓe isa wasu wurare cikin aminci, kawo cikas ga jigilar kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, tare da rage damar masu zaɓe na fita domin kaɗa ƙuri’unsu.

Kara karanta wannan

To fa: ADC ta fallasa makarkashiyar da ake shiryawa kan zaben 2027, ta ja kunnen Tinubu

Amupitan ya ce ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumar zaɓe da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen bai wa ’yan Najeriya damar amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya ba tare da tsoro ko barazana ba.

Ya ƙara da cewa ɗaukar mataki da wuri, tura jami’an tsaro yadda ya kamata da kuma mayar da martani cikin haɗin kai ga barazanar tsaro su ne muhimman matakan da za su taimaka wajen kare sahihanci, haɗa kan al’umma da kuma zaman lafiyar zaɓen 2027.

Amupitan ya yi maganar zaben 2027
Farfesa Joash Amupitan na jawabi a wajen taro Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Majalisa ta gayyaci shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta gayyaci shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

Majalisar wakilan ta gayyaci Amupitan ne domin ya yi bayani kan shirye-shiryen hukumar na gudanar da babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng