Dan Atiku ya Faɗi dalilin Fanɗarewa Ubansa, Ya Ɗauki Alƙawari ga Tinubu

Dan Atiku ya Faɗi dalilin Fanɗarewa Ubansa, Ya Ɗauki Alƙawari ga Tinubu

  • Abba Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai tabbatar da Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Adamawa
  • Ɗan Atiku ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu ba yana nufin yana adawa da mahaifinsa ko burinsa na siyasa ba
  • Abba ya yaba da manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, inda ya ce shirye-shiryen gwamnati sun taimaka wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Abba Abubakar, ɗan Atiku Abubakar, ya yi magana kan bambancin ra'ayi na siyasa tsakaninsu.

Abba ya ce zai tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a Adamawa, jihar mahaifinsa, a zaɓen 2027.

Dan Atiku ya yi wa Tinubu alkawari
Abba Atiku yayin kaddamar da tafiyar Bola Tinubu a Adamawa. Hoto: Abba Atiku.
Source: Facebook

Dan Atiku ya kafa tubalin kamfen Tinubu

Abba ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja, yayin ƙaddamar da ƙungiyar Haske Bola Tinubu Organisation (HBTO), cewar Punch.

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya kaddamar da gagarumin shiri don tazarcen Tinubu a 2027

An kuma ƙaddamar da shirin tallafa wa jama'a wajen sufuri da rangwamen kuɗin mota a wajen taron.

Abba, wanda ya kafa HBTO, ya ce matakin da ya ɗauka na goyon bayan Tinubu ba wani yunƙuri ba ne na tayar da hankali tsakanin shi da mahaifinsa, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC.

Ya ce:

"Na fahimci cewa matakan siyasa, musamman waɗanda suka bambanta da ra'ayin mutanen da mutum yake da alaƙar iyali da su, kan jawo hankalin jama'a sosai.
"Sai dai imanin siyasa ya danganta ne da ra'ayin mutum, lamirinsa da kuma 'yancin kowa na yin zaɓin kansa.
"Matakin da na ɗauka na kafa da jagorantar HBTO zaɓin siyasa ne da na yi da gangan, bisa cikakken imani da alkiblar da muka zaɓa."

Ya ce dimokuraɗiyya tana ƙara ƙarfi idan mutane suna da 'yancin yin zaɓin siyasa, tattaunawa mai ma'ana da kuma goyon bayan shugabanni da jam'iyyun da suka yi imanin za su cimma burinsu..

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Abba ya yaba da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta kawo, inda ya ambaci Asusun Tallafin Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) da zuba jari kan manyan ayyukan more rayuwa.

Ya kuma ambaci ƙarin kuɗaɗen da ake warewa gwamnatocin jihohi da shirye-shiryen tallafa wa jama'a wajen sufuri a matsayin wasu muhimman tsare-tsaren jin ƙai na gwamnati.

Sai dai ya ce bai kamata a fassara matakin da ya ɗauka a matsayin cin amanar dangantakar iyalinsa ko burin mahaifinsa na siyasa ba.

Da aka tambaye shi ko zai tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya samu ƙuri'u masu yawa a Adamawa, Abubakar ya amsa da cewa:

"Eh, eh, eh. Za mu tabbatar da nasarar APC a Adamawa.
"Na kasance ina goyon bayan mahaifina tun lokacin da na fara shiga harkokin siyasa, kuma na goya masa baya saboda abubuwan da ya yi wa ƙasar nan. "Amma na yi imanin cewa duk lokacin da gwamnati ta fito da manufofin da za su taimaka wa jama'a, zan mara mata baya."

Tinubu ya jawo yi wa malami ihu

Mun baku labarin cewa rikici ya barke a wani masallaci a Taraba bayan wani mai ibada ya kalubalanci Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo kan gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

Sheikh Jalo Jalingo ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta zaluntar jama'a, amma wani mai sallah ya fito ya ce karya yake yi.

Malamin ya bukaci al'ummar Taraba su yi hakuri, su zabi APC a 2027, inda wasu masu amfani da Facebook suka soki matsayinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.