Na Gaban Goshin Tinubu Ya Fadi Wa Suke Shakka a 2027, Banda Atiku da Obi
- Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari ya ce ba sa tsoron ’yan hamayya irin su Atiku Abubakar ko Peter Obi
- Masari ya bayyana cewa ba su dauki Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wata barazana ba, sun kallon shi a matsayin dan wasan kwaikwayo
- A hirar da aka yi da shi game da zaben 2027, Masari ya bayyana wadanda shugaban kasa Tinubu ke jin shakka yayin da ake tunkarar zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCt, Abuja - Manyan 'yan siyasar Najeriya na cigaba da bayanai kan shirye-shiryen da suke yi gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya bayyana cewa a yanzu haka ba su jin tsoron kowa.

Source: Facebook
Masari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da TRT Hausa da tashar ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma'a, 12 ga Nuwamban 2026.
Maganar tsoron Atiku a 2027
Ibrahim Masari ya bayyana cewa a shirin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a 2027, ba ya jin tsoron wani dan takarar jam'iyyar adawa.
Da aka tambaye shi game da Atiku Abubakar da ake cewa suna jin tsoro, hadimin shugaban kasar ya ce:
'Idan kana jin tsoron Atiku ashe kana jin tsoron matarka." Ni abin da na sani Allah shi ne abin tsoro, kuma shi muke jin tsoro."
Masari ya kara da cewa Atiku Abubakar ba shi da wani abu sabo da zai kalli 'yan Najeriya ya fada masu domin su zabe shi a 2027.
Magana kan Obi da Kwankwaso
Da ya dawo kan jam'iyyar NDC, Ibrahim Masari ya bayyana cewa ba su jin fargabar Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan
Gwamna ya jero dalilai 4 da suka sa zai yaƙi Tinubu a 2027 duk da ya goyi bayansa a 2023
A game da Kwankwaso, Masari ya ce:
"Wannan ai dan wasan kwaikwayo ne. Ba a sa shi a lissafi."
Game da wanda suka fi jin shakkam Masari ya bayyana cewa:
"Na gaya naka, na fi tunanin talaka, menene korafin talaka,"
Hadimin shugaban kasar ya ce shugaban Bola Tinubu ya fi kwanciya ya ta shi da korafin talaka a kan abokan hamayyar shi kamar Peter Obi da Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Maganar hadakar 'yan adawa
Masari ya bayyana cewa ba su shakkar hadakar da ake cewa 'yan adawa za su yi a Najeriya domin kifar da Bola Tinubu.
Ya ce a shirye suke su tunkari kowace irin hadaka 'yan jam'iyyar ADC, NDC da zauransu za su yi kafin zaben shugaban kasa na 2027.
"Ni ban ma san me suke yi ba, ko su hada kai, ko kar su hada kai, mu a wajen Allah muke nema."
Maganar Nafi Bala na NDC
A wani labarin, kun ji cewa Nafiu Bala da ke ikirarin zama shugaban jam'iyyar ADC ya ce ya amince da salon tafiyar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso
Ya ce 'yan adawa na samun damar gudanar da harkokin su lafiya a Najeriya, kuma ba shi da wani korafi da zai gabatar a kan Tinubu.
A wata hira da aka yi da shi, Nafiu Bala ya bayyana cewa shi bai yarda da yadda ake sukar Bola Tinubu da sunan adawa ba.
Asali: Legit.ng
