Hukunci kan Kirista da Ta Cire Wata a Musulunci Ya Raba kan Kiristoci

Hukunci kan Kirista da Ta Cire Wata a Musulunci Ya Raba kan Kiristoci

  • Kungiyar PFN da lauyoyin Kirista sun bukaci mabiya addinin Kirista su yi taka-tsantsan kan hukuncin da aka yanke wa Lami Samuel Dawa a Borno
  • An yankewa Lami Dawa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa zargin hana mahaifi kula da diyarsa, ba wai wa'azin Kiristanci kadai ba
  • CLASFON ta bayyana cewa an daukaka kara kan hukuncin, yayin da PFN ta bukaci jama'a su guji yada bayanan da ba a tabbatar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) da Kungiyar Lauyoyin Kirista ta Najeriya (CLASFON) sun shawarci Kiristoci kan zaman lafiya.

Kungiyoyin sun bukaci 'yan Najeriya, musamman Kiristoci, su kwantar da hankulansu kan hukuncin da aka yanke wa wata Kirista, Mrs Lami Samuel Dawa.

An daure wata Kirista a gidan yarin Borno
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

An yanke wa Lami hukunci

Kara karanta wannan

Alfarmar da shugabannin Arewa suka nema daga Tinubu saboda zaɓen Buhari

Rahoton Punch ya ce kotu ta yankewa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari a jihar Borno.

An samu Dawa da laifi, inda aka yanke mata hukuncin daurin shekaru 14 bisa zargin yi wa wata yarinya Musulma wa'azi, wadda rahotanni suka ce ta musulunta zuwa Kiristanci.

Rahotanni sun bayyana cewa Mai shari'a A. B. Kumdila na Babbar Kotun Jihar Borno ne ya yanke mata hukuncin bisa sashe na 210 na dokar Penal Code ta jihar.

Hukuncin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu Kiristoci suka bayyana shi a matsayin nuna wariya ga addininsu, tare da kira ga kungiyoyin Kirista su shiga lamarin.

Sai dai PFN da CLASFON sun yi gargadin yada bayanan da ba a tantance ba game da shari'ar, suna masu cewa al'amuran da suka kai ga hukuncin sun fi yadda ake bayyanawa jama'a sarkakiya.

Da yake zantawa da manema labarai, Sakataren PFN na kasa, Bishop David Bakare, ya ce kungiyar ta samu labarin shari'ar, amma bayanan da ake yadawa ba su bayyana hakikanin abin da ya faru ba.

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo ɗauki mai zafi, manyan 'yan ta'adda sun fara guduwa a Najeriya

Ya gargadi Kiristoci da su guji kalaman tunzura jama'a da yanke hukunci ba tare da nazarin yadda shari'ar ta gudana a kotu ba.

Bakare ya ce:

“An sanar da PFN game da shari'ar, amma bincikenmu ya nuna cewa ba ta kasance kamar yadda ake yadawa a bainar jama'a ba. Don haka ina shawartar masu magana kan lamarin su gudanar da cikakken bincike.
“Muna taka-tsantsan, ba ma son mu bi shari'a kawai ba tare da sanin cikakken bayani ba. Ba ma son mutane su yi mana kallon jahilai.”

Ya bayyana cewa kungiyar na bibiyar shari'ar, yana mai cewa sun ji dadin samun daukaka kara kan hukuncin da aka yanke wa Dawa.

An yanke wa wata Kirista hukuncin zuwa gidan yari
Lami Samuel Dawa da aka tura gidan yari da sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

A nasa bangaren, Shugaban reshen CLASFON na Maiduguri, Ephraim Yidawi, ya bukaci Kiristoci su kwantar da hankulansu tare da guje wa yada bayanan shari'ar da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Yidawi ya bayyana cewa kungiyar lauyoyin ta wakilci Dawa da wasu mutane hudu a lokacin shari'ar, inda aka samu Dawa da laifi, amma kotu ta wanke sauran mutum hudun.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fusata kan kisan Sheikh Masussuka, sun aika sako ga gwamnati

Ya yi gargadin cewa bai kamata a takaita shari'ar da ikirarin cewa an hukunta Dawa ne kawai saboda yi wa yarinya karamar shekaru wa'azi ko shigar da ita Kiristanci ba.

A cewarsa, ana tuhumar wadanda ake kara da laifukan hada baki wajen sace yaro, yaudara ko jawo yaro ya bar gidan iyayensa, da kuma cire shi daga hannun iyayensa ba bisa ka'ida ba.

Sauran tuhume-tuhumen sun hada da hana yaron samun damar zuwa makaranta da kuma katsalandan a harkokin addininsa da sauya addininsa zuwa Kiristanci.

Dan agaji: Kiristocin Arewa sun magantu

An ji cewa Rabaran John Joseph Hayab ya bukaci ’yan sanda su kama duk wadanda ke da hannu a bidiyon barazanar kashe Kiristoci a Zamfara.

Hayab ya yaba wa ’yan sanda bisa kama wani wanda ake zargi, amma ya ce dole a binciki duk wadanda suka shiga lamarin ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Shugaban Kiristocin ya bukaci Kiristoci kada su bari bidiyon ya tsorata su, yayin da ya yi kira ga shugabannin addinai su ci gaba da tattaunawa domin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.