Abokin Takarar Pantami a Gombe Ya Bukaci Kowane Dan APC Ya Kawo Akwatinsa

Abokin Takarar Pantami a Gombe Ya Bukaci Kowane Dan APC Ya Kawo Akwatinsa

  • Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya yi kira ga 'yan jam'iyyar su dage wajen tallata shi gabanin zaben 2027
  • Jamilu Gwamna ya bayyana cewa duk wanda ya gaza kawo akwatin mazabar shi ba zai kasance tare da shi ba bayan kafa gwamnati
  • Ya kuma yi kira ga 'yan jam'iyyar APC su tabbatar sun samawa shugaban kasa Bola Tinubu kuri'a sama da miliyan 1 a zaben da za a yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya bayyana cewa ba zai lamunci rashin hada kan jama'a ba.

Ya bayyana cewa dole duk wanda yake so a dama da shi a gwamnatin shi ya dage da neman jama'a ta yadda zai iya kawo akwatinsa a 2027.

Kara karanta wannan

Ruɗani: INEC ta ɗora NDC amma babu sunan Aminu Gwarzo a jerin 'yan takarar gwamnan Kano

Jamilu Isiyaku Gwamna
Dan takarar APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna. Hoto: Dr Jamil Gwamna
Source: Facebook

A wani bidiyo da shafin Gombe Reporters ya wallafa a Facebook, Jamilu ya yi kira ga 'yan APC da su tabbata sun samawa shugaba Bola Tinubu kuri'u masu yawa.

Maganar kawo akwati a 2027

Yayin da yake magana a wajen wani taro, Dr Jamilu Gwamna ya bayyana cewa ba zai lamunci mutane su rika saka babbar riga suna nuna cewa sune a gaba-gaba ba tare da neman jama'a ba.

Ya tabbatar da cewa wadanda suka kawo akwatinsu ne kawai za su kasance tare da shi idan Allah ya ba shi nasara a zaben 2027.

Ya ce:

"Ni ba zan yarda da wannan ba, abin da zan muku alkawari shi ne, wallahi komai kusancin ka da ni, idan baka kawo mazabar ka ba, baruwan da kai, ba ruwa na da kai. Idan baka min ba, ba zan maka ba."

Dan takarar ya bayyana cewa shi ma idan ya samu kuri'un ne zai samu damar zuwa Abuja ya nemawa Gombe alfarma domin kawo ayyukan cigaba.

Kara karanta wannan

An yi wa Shehin malamin Musulunci rashin kunya a masallaci saboda Tinubu

Maganar zaben Tinubu a 2027

Jamilu Gwamna ya bayyana cewa burin APC a jihar Gombe shi ne samawa shugaban kasa Bola Tinubu sama da kuri'a miliyan 1.

Ya bayyana cewa matukar za a samawa shugaba Bola Tinubu kuri'a miliyan 1, shi ko kasa da haka ya samu ba babu damuwa.

Ya kara da cewa idan mutanen Gombe suka zabi Tinubu da kuri'u masu yawa zai je har Abuja ya nemawa Gombe ministoci 2 a gwamnatin da Tiubu zai kafa bayan 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dan takarar ya bayyana cewa a 2023 da mutanen Bauchi suka ba shugaba Tinubu kuri'u masu yawa ya ba su ministoci biyu a gwamnatinsa.

Bayanin lauyan Pantami

A wani labarin, kun ji cewa wasu rahotani sun nuna cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dawo da Sheikh Isa Ali Pantami cikin 'yan takara.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta game da makomar siyasar jihar Gombe, inda wasu ke cewa akwai sauran aiki har yanzu.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sheikh Pantami, Barista Ibrahim Attahir ya bayyana cewa su ga Allah suka dogara kuma suna da nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng