Sanata Okorocha Ya Tona wa Gwamnan APC Asiri, Ya Ce Bai Taba Cin Zabe a Tarihinsa ba

Sanata Okorocha Ya Tona wa Gwamnan APC Asiri, Ya Ce Bai Taba Cin Zabe a Tarihinsa ba

  • Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya ce Sanata Hope Uzodinma bai taɓa lashe zaɓe ba a rayuwarsa
  • Ya yi wannan furuci ne bayan kotu ta soke nasarar Uzodinma a zaɓen fitar da gwani na APC na takarar sanata
  • Okorocha ya ce shi ne ya lashe tsaida fidda gwani, kuma tun can da magudi gwamnan Imo yake cin takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya caccaki Mai girma Hope Uzodinma da ya karbe takarar sanata a hannunsa.

Sanata Rochas Okorocha ya ce Gwamnan Imo bai taɓa lashe wani zaɓe a rayuwarsa ba duk da irin mukaman da ya rike a tarihi.

Rochas
Sanata Rochas Okorocha da Gwamnan Imo a taron siyasa Hoto: Senator Rochas Okorocha/Hope Uzodinma
Source: Facebook

Da Channels ta yi hira da shi, Rochas Okorocha ya yi kaca-kaca da Hope Uzodinma bayan nasarar da ya samu a kan shi a kotu.

Kara karanta wannan

Sanata Okorocha ya wuce girman gwamna, ya ce shi ne jagoran jam'iyyar APC gaba daya

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Okorocha ya ce Uzodinma bai taɓa lashe wani zaɓe ba, yana zarginsa da murdiya.

Ya ce ya yi ta samun nasarorin siyasa ne ta hanyar maguɗin sakamakon zaɓe da rubuta sakamako.

Okorocha ya ce:

“Hope bai taɓa lashe wani zaɓe ba a rayuwarsa. Ku koma baya ku duba. A gaskiya, abin da yake yi shi ne ya shiga daki wani ya rubuta sakamako, irin yadda ya yi a zaben tsaida gwanin APC
Yau sakamakon zaben da ya kawo, mutum daya ya rubuta su

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa nasarorin Uzodinma a zaɓe sun samo asali ne daga rubuta sakamakon ƙuri'u na bogi kurum.

Okorocha wanda ya yi gwamna ya ce haka Uzodinma yake yi ya samu mulki maimakon bin ainihin zaɓin masu kaɗa ƙuri'a.

Nasarorin Gwamna Hope Uzodinma a baya

Ya kuma yi nuni da wasu rigingimun zaɓe da suka shafi Uzodinma a baya, yana mai cewa takardun kotu sun shaida magudinsa

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

‘Dan siyasar ya ce hakan ba yana nufin suna goyon bayan gwamnan ba ne, sai dai an kududune alkalai ne, babu yadda suka iya.

A cewarsa, wani ne ya rubuta sakamakon zaben rumfuna 388 da ake takarar gwamna, sai kotu ta soke wadannan kuri'u.

Okorocha ya ce ganin babu wanda ya kalubalanci wannan a kotu, ta haka Uzodinma ya zama gwamna daga na hudu a zabe.

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa an maimaita irin wannan abu a zaɓen tsaida gwani na APC na mazabar sanatan Imo ta Yamma.

Hakan ya haifar da takaddamar shari'a kan wanda ya cancanci zama ɗan takarar jam'iyyar mi mulki a zabe mai zuwa na 2027.

Rochas Okorocha ya ji dadin hukuncin kotu

Leadership ta rahoto shi yana cewa Uzodinma ya ɗauka cewa shi ne zai zama ɗan takarar jam'iyyar duk da an yi karar shi a kotu.

Tsohon gwamnan ya kuma nuna farin cikinsa da hukuncin kotun ranar Alhamis, yana cewa hakan ya nuna ba a sayen shari’a a kasa.

Ya ce:

“Na yi farin ciki da ganin cewa yanzu ba za a iya sayen shari'a ba. Ba a sayar da ita ga wanda ya fi kowa kuɗi.”

Kara karanta wannan

Kotu ta karbe takarar gwamna Uzodinma amma jam’iyyar APC ta yi mursisi

Okorocha ya ce hukuncin ya tabbatar da matsayinsa kan takaddamar zaɓen tsaida gwanin, ya ce takardun bogi Uzodinma ya ƙirƙira.

Hadimin shugaban APC na kasa, Imran Muhammad ya daura bidiyon hirar a shafinsa na X.

Rikicin Okorocha da Gwamnan Imo

Tun tuni aka ji labari Rochas Okorocha ya yi zargin cewa Gwamnan jihar Imo yana yi masa makarkashiya don hana shi takarar shugaban kasa.

Okorocha ya jaddada cewa babu wani abu da zai hana shi yin takarar, tare da bayyana cewa har yanzu shi cikakken dan jam'iyyar APC ne a Imo.

Sai dai gwamnan na Imo, Hope Uzodinma ya bukace shi da ya kyale shi ya jagoranci jihar a cikin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng