Abu Ya Girma: Fada Ta Kaure Tsakanin Okorocha da Gwamna kan Takarar Sanata

Abu Ya Girma: Fada Ta Kaure Tsakanin Okorocha da Gwamna kan Takarar Sanata

  • Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya maka INEC, Hope Uzodimma da APC ƙara a kotu
  • Okorocha ya ce shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na APC, inda ya samu ƙuri’u 150,780, yayin da Uzodimma ya samu 102,158
  • Ya bukaci kotu ta soke sunan Uzodimma, sannan ta umarci INEC ta amince da shi a matsayin ɗan takarar APC na Imo ta Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ƙara a kotu.

Okorocha ya dauki wannan mataki ne yana neman bahasi bayan an wallafa sunan Hope Uzodimma a matsayin ɗan takarar APC.

Okorocha ya maka gwamna Uzodinma a kotu
Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha. Hoto: Rochas Okorocha.
Source: Twitter

Uzodimma, wanda shi ne gwamnan Imo, an bayyana shi a matsayin ɗan takarar APC na yankin Sanatan Imo ta Yamma gabanin babban zaɓen 2027, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Okorocha ya hada APC, gwamna da INEC ya maka a kotu kan takarar sanata

Wadanda Okorocha ke kara

Sauran waɗanda aka shigar da su cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1854/2026 sun haɗa da Uzodimma da jam’iyyar APC.

A cewar NAN, lauyan Okorocha, O.J. Aboje, ya shigar da takardar ƙarar a ranar 13 ga watan Agustan 2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Okorocha ya kasance gwamnan Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019, sannan ya zama Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma daga shekarar 2019 zuwa 2023.

A watan Mayu, ya fafata da Uzodimma domin samun tikitin APC na yankin Sanatan Imo ta Yamma gabanin zaɓen 2027.

Williams Kayode, shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a Imo, ya bayyana Uzodimma a matsayin wanda ya yi nasara.

Kayode ya ce Uzodimma ya samu ƙuri’u 230,464 a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar domin tantance ɗan takarar jam’iyyar.

An maka Uzodinma a kotu
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma. Hoto: Hope Uzodinma.
Source: UGC

Ƙarar da Rochas Okorocha ya shigar

Okorocha ya bukaci kotu ta tantance ko INEC ba ta da hurumin bin rahotannin jami’anta da suka sanya ido kan zaɓen fidda gwani na APC.

Kara karanta wannan

Akwai kura: INEC ta lissafo abubuwan da ke barazana ga zaben 2027

An gudanar da zaɓen fidda gwamin ne a ranar 18 ga Mayu domin zaɓen ɗan takarar APC na yankin Sanatan Imo ta Yamma, cewar Punch.

Tsohon gwamnan ya bukaci kotu ta bayyana cewa wallafa sunan Uzodimma a matsayin ɗan takarar APC bai dace da Kundin Tsarin Mulki ba.

Ya kuma nemi kotu ta soke sanarwar INEC da ta bayyana Uzodimma a matsayin ɗan takarar da ya samu mafi yawan ƙuri’u a zaɓen fidda gwani.

Rochas ya kuma nemi kotu ta hana Hope Uzodimma, APC ko wani mutum bayyana shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen Sanatan Imo ta Yamma.

Amen Rochas, ɗan tsohon gwamnan, ne ya rattaba hannu kan rantsuwar da aka haɗa da ƙarar, inda ya bayyana wasu bayanai game da lamarin.

Ya ce Uzodimma, wanda wa’adinsa ba zai ƙare ba kafin fara zaman Majalisar Dattawa a 2027, ya sayi fom ɗin neman tikitin APC.

Uzodinma zai koma majalisar dattawa

A baya, an ji cewa Gwamnan Imo zai nemi ya koma majalisa Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana aniyarsa ta takarar kujerar Sanatan Imo ta Yamma.

Kara karanta wannan

Abin da ADC ta yi da ya taimaka wajen kayar da jam'iyyar APC a zaben gwamnan Osun

Ana cewa gwamnan yana shirin murabus daga mukaminsa na gwamna domin ya dare kan wannan kujera ta Majalisar dattawa a shekarar badi.

Wasu rahotanni na nuni da cewa gwamnonin jam'iyyar APC na goyon bayan wannan mataki domin ganin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.