2027: Kotu Ta Rusa Takarar Shugaban Gwamnonin APC na Najeriya

2027: Kotu Ta Rusa Takarar Shugaban Gwamnonin APC na Najeriya

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma a zaɓen 2027
  • Kotun ta yanke hukuncin cewa tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ne ya lashe mafi yawan ƙuri’u a zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a ranar 18 ga Mayu
  • Alƙali Obiora Egwuatu ya umarci APC da ta miƙa sunan Okorocha ga INEC a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Imo ta Yamma a babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma.

Kara karanta wannan

An fara gano kura kurai a shirin zaben 2027, Kwankwaso ya gargaɗi INEC

Mai Shari’a Obiora Egwuatu ne ya bayar da umarnin a ranar Alhamis, bayan ya yanke hukuncin cewa Uzodinma bai lashe zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a ranar 18 ga Mayu ba.

Hope Uzodimma
Gwamna Hope Uzodimma yana jawabi. Hoto: Imo State Governor
Source: Facebook

Kotu ta ce Okorocha ne ya ci zaɓen

A hukuncin da ya yanke, Punch ta ce alƙalin ya ce hujjojin da aka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ne ya samu mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen fidda gwani.

Zaɓen dai an gudanar da shi ne ƙarƙashin kulawar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Kotun ta bayyana cewa sakamakon zaɓen ya nuna cewa Okorocha ne ya kamata a amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Za a miƙa sunan Okorocha ga INEC

Bayan yanke hukuncin, Mai Shari’a Egwuatu ya umarci APC da ta miƙa sunan Okorocha ga INEC a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Imo ta Yamma a babban zaɓen 2027.

Kotun ta kuma umarci Uzodinma da ya dakatar da gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na wannan kujera.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Channels TV ta wallafa cewa ukuncin ya shafi takarar kujerar sanatan Imo ta Yamma, wadda za a fafata a zaɓen da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Hukuncin ya zo ne yayin da jam’iyyun siyasa da ’yan takara ke ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027, tare da wasu takaddama kan sakamakon zaɓen fitar da gwani da jerin sunayen ’yan takara.

Maganar takarar Pantami da sauransu

A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta ce za ta yanke shawara kan makomar tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, da Ladi Adebutu, da wasu ’yan siyasa.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ya bayyana hakan a wata hira a ranar Laraba, inda ya ce hukumar za ta tattauna batun a taronta na ranar Alhamis.

Pantami na neman kujerar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin PDP, yayin da Adebutu ke neman kujerar gwamnan Ogun a ƙarƙashin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng