Sanata Ya Wuce Girman Gwamna, Ya Ce Shi Ne Jagoran Jam’iyyar APC Gaba Daya
- Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya yi ikirarin cewa har yanzu shi ne jigon APC kuma mai tasiri a siyasar jam’iyyar
- Okorocha ya ce shi ne ya taimaka wajen kafa APC, har ma ya taka rawa wajen samar da sunan jam’iyyar
- Ya yi watsi da masu ikirarin adawa da shi, yana mai cewa babu wani zaɓen cikin gida da ya tabbatar da shugabancinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi watsi da ikirarin cewa ya rasa iko da tsarin jam’iyyar APC a jihar.
Okorocha ya jaddada cewa har yanzu yana da muhimmiyar rawa wajen tafiyar da jam’iyyar, tun daga kafa ta har zuwa tsarin siyasar ta a Imo.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News ranar Alhamis, inda ya yi magana kan rikicin cikin gida na APC.
Okorocha ya ce shi ne APC a Imo
Tsohon gwamnan ya yi watsi da ikirarin cewa wasu masu fada a ji a APC suna ƙoƙarin kawar da shi daga tsarin jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Imo ta Yamma.
Zaɓen fidda gwanin na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen 2027, inda yake takun saƙa da Gwamna Hope Uzodimma kan tikitin takarar sanatan.
Okorocha ya ce:
“Rochas shi ne APC a jihar Imo. Ni ne ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa wannan jam’iyya.
“Tsarin APC a jihar Imo Rochas ne. Kuma ni ne na ba jam’iyyar sunan APC.”

Source: Facebook
Okorocha ya kuma yi watsi da rahotannin cewa gwamnatin jihar Imo na shirin ƙalubalantar hukuncin kotun da ta amince da nasararsa.
Ya tambayi dalilin da zai sa gwamnatin jihar ta shiga takaddama tsakaninsa da Gwamna Hope Uzodimma kan tikitin takarar sanata.

Kara karanta wannan
Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki
Ya ce:
“Me ya haɗa gwamnatin jihar Imo da zaɓen da ke tsakanina da Hope Uzodimma a matsayinsa na mutum? Ba gwamnatin jihar Imo ce ke takara ba, Hope Uzodimma ne.”
Ya yi magana kan tasirinsa a zaɓen 2027
Okorocha ya ce takaddamar ba ta nuna ƙarfin APC a jihar Imo ba, sai dai rashin jituwa kan wanda zai isar da saƙon siyasar jam’iyyar ga masu zaɓe.
Ya bayyana cewa kyakkyawar alaƙarsa da al’ummar jihar na ba shi damar tara goyon baya ga APC da Shugaba Bola Tinubu gabanin zaɓen 2027.
Kotu ta tabbatar wa Uzodinma takara
Mun ba ku labarin cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma a zaɓen 2027.
Kotun ta yanke hukuncin cewa tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ne ya lashe mafi yawan ƙuri’u a zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a ranar 18 ga Mayu.
Alƙali Obiora Egwuatu ya umarci APC da ta miƙa sunan Okorocha ga INEC a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Imo ta Yamma a babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
