Yadda Pantami Ya Tsallake Tarko Ya Shiga Takara bayan Korafi 69 ga INEC
- Hukumar INEC ta amince da ƙorafe-ƙorafe 41 cikin 69 da aka shigar kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027, yayin da ta yi watsi da 28
- Hukumar ta ce ƙorafe-ƙorafen sun fito ne daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26, inda wasu suka shafi cire sunayen ’yan takara da sauransu
- INEC ta tabbatar da cewa an amince da maido sunayen wasu ’yan takara da aka cire a baya, ciki har da Farfesa Isa Ali Pantami na PDP a Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da ƙorafe-ƙorafe 41 cikin 69 da aka shigar kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027, yayin da ta yi watsi da sauran 28.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, INEC ta amince da takarar Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo a zaɓen 2027
Shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis.

Source: Twitter
Rahoton Vanguard ya nuna cewa Kudu Haruna ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen sun fito ne daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26 na ƙasar.
Dalilan shigar da ƙorafe-ƙorafen
Haruna ya ce ƙorafe-ƙorafen sun shafi cire sunayen wasu jam’iyyun siyasa daga jerin ’yan takara, shigar da sunayen ’yan takarar da ba su cikin rajistar mambobin da jam’iyyunsu suka gabatar, da kuma zargin tsayar da mutum a matsayin ɗan takara fiye da sau ɗaya.
Ya bayyana cewa hukumar ta duba ƙorafe-ƙorafen tare da bayanan da ke hannunta da kuma tanade-tanaden dokokin da suka shafi zaɓe kafin yanke hukunci.
A cewarsa, bayan nazarin ƙorafe-ƙorafen, hukumar ta ga cewa wasu suna da hujja, don haka ta amince a shigar da sunayen ’yan takara da jam’iyyun da abin ya shafa cikin jerin.
Sai dai wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa hukumar ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da ta ga ba su da hujja.
Haruna ya ƙara da cewa:
“Bayan nazarin ƙorafe-ƙorafen, bayanan da suka dace da kuma tanade-tanaden dokoki, hukumar ta ga cewa wasu ƙorafe-ƙorafe suna da hujja, ta kuma amince a shigar da sunayen ’yan takara da jam’iyyunsu da abin ya shafa, yayin da ta yi watsi da waɗanda ba su da hujja.
“Bugu da ƙari, an cire wasu sunaye da aka saka ba bisa ƙa’ida ba cikin jerin ƙarshe bayan tabbatar da cewa ba su cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu.
“Hukumar ta kuma amince da cire ’yan takarar da aka gano cewa tsayar da su bai dace da tanade-tanaden dokokin da suka dace ba.”

Source: Facebook
Isa Pantami ya samu damar takara
Ko da yake INEC ba ta bayyana sunayen ’yan takarar ko jihohin da abin ya shafa a sanarwar ba, wata majiya ta bayyana cewa hukumar ta amince da takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a Gombe.
Majiyar ta kuma ce an amince da takarar Abdulsalam Gwarzo, ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a jihar Kano, bisa jiran sakamakon shari’o’in da ke gaban kotu.
a dukule, INEC ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 61 daga jam’iyyun siyasa 11 a jihohi 11 kan jerin sunayen ’yan takarar majalisun dokokin jihohi.
An taya Sheikh Isa Pantami murna
A wani labarin, kun ji cewa al’ummar jihar Gombe sun fito kan tituna cikin dare domin murnar dawo da sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar na zaɓen 2027.
Masu goyon bayan Pantami sun yi jerin gwanon motoci da babura a unguwannin Pantami, Jekadafari da sauran sassan birnin Gombe.
Wani mai goyon bayan ADC ya bayyana farin cikinsa da dawo da sunan Pantami, yana mai cewa hakan na iya rage ƙuri’un APC da PDP.
Asali: Legit.ng

