2027: Ɗiyar Tinubu Ta Yi Maganar da ka Iya Tsorata Yan Najeriya kan Atiku da Peter Obi

2027: Ɗiyar Tinubu Ta Yi Maganar da ka Iya Tsorata Yan Najeriya kan Atiku da Peter Obi

  • Mujidat Folasade Tinubu-Ojo ta ƙaddamar da ƙungiyar Iyaloja General Movement (IGM) tare da alƙawarin tara wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan 10
  • Ta buƙaci ’yan Najeriya kada su zaɓi Atiku Abubakar da Peter Obi, tana mai cewa za su mayar da ƙasar baya
  • Tinubu-Ojo ta ce an kafa tsare-tsare a jihohi 36, ƙananan hukumomi da unguwanni domin tattara goyon bayan ’yan kasuwa da masu zaɓe a matakin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mujidat Folasade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuma Iyaloja-Janar ta Najeriya, ta ƙaddamar da ƙungiyar Iyaloja General Movement (IGM).

Ɗiyar shugaban kasar ta yi alƙawarin samo wa mahaifinta da jam’iyyar APC ƙuri’u miliyan 10 a babban zaben 2027.

Yar Tinubu
Mujidat Folasade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuma Iyaloja-Janar ta Najeriya Hoto: Iyaloja General TV
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa an ƙaddamar da ƙungiyar ne ranar Alhamis a Eagle Square da ke Abuja, a wajen wani taro da ya samu halartar dubban shugabanni da magoya baya.

Kara karanta wannan

Yadda Pantami ya tsallake tarko ya shiga takara bayan korafi 69 ga INEC

Yadda aka tsara tafiyar ɗiyar Tinubu

Ta kuma buƙaci ’yan Najeriya kada su zaɓi Atiku Abubakar da Peter Obi, ’yan takarar jam’iyyun adawa, tana mai cewa za su iya rusa nasarorin da aka samu tare da mayar da Najeriya baya.

Tinubu-Ojo ta ce sun samar da tsare-tsare a jihohi 36, ƙananan hukumomi da mazabu domin tattara matan kasuwa, ’yan kasuwa da sauran masu zaɓe a matakin ƙasa don goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Da take jawabi ga mahalarta taron, Tinubu-Ojo ta ce an kafa IGM ne domin wayar da kan shugabannin kasuwanni da masu sana’o’in hannu da sauran waɗanda ke aiki a ɓangaren tattalin arziki.

Ɗiyar Tinubu ta soki Atiku, Obi

Iyaloja-Janar ɗin ta bayyana mata da maza masu sana’a a kasuwanni a matsayin gungun masu zaɓe masu tasiri, waɗanda ’yan siyasa ba za su iya yin biris da su ba.

Ta kuma shawarci ’yan Najeriya da kada su yi la’akari da shugabannin jam’iyyun adawa da ’yan takarar shugaban ƙasa irin su Atiku Abubakar da Peter Obi, tana mai cewa za su mayar da ƙasar baya.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

“Abin da muke ƙoƙarin cimmawa a matsayin shugabannin kasuwanni shi ne ƙarfafa mutanenmu, wayar musu da kai kan zaɓe mai zuwa da kuma hanyar da ya kamata su bi,” in ji ta.

Ta kare manufofin Tinubu

Da take kare gwamnatin yanzu da manufofinta, Tinubu-Ojo ta ce shugaban ƙasar ya ƙaddamar da matakai waɗanda daga ƙarshe za su inganta tattalin arzikin Najeriya, innji rahoton Punch.

Obi Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da takwaransa na ADC, Atiku Abubakar Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ta ƙara da cewa ƙalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu wani ɓangare ne na sauyin da ke da wahala, amma alfanun matakan za su ƙara bayyana yayin da lokaci ke tafiya.

“Abin da yake yi a yanzu tamkar mace mai juna biyu ce da ke fama da naƙuda. Muna cikin wannan wahalar a yanzu, kusan dukkan ’yan Najeriya suna jin tasirin abin da yake yi, manufofin suna da zafi, amma sakamakon ƙarshe zai tabbatar da cewa matakan sun dace,” in ji ta.

An bukaci Atiku ya jingine siyasa

Kun ji cewa Alwan Hassan ya bukaci Atiku Abubakar ya yi ritaya daga siyasa maimakon sake neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027

Jigon na APC ya zargi Atiku da kasa samar da ci gaba mai ma’ana a Arewacin Najeriya duk da shekarun da ya yi a manyan muƙaman gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262