APC Ta Fito da Magana kan Zargin Ministoci na Biyan Biliyoyi don Samun Mukami

APC Ta Fito da Magana kan Zargin Ministoci na Biyan Biliyoyi don Samun Mukami

  • APC ta yi magana kan kalaman kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓenta, Alwan Hassan, game da biyan biliyoyin naira domin samun muƙaman ministoci
  • Kakakin yaɗa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce Alwan Hassan ya bayyana cewa yana magana ne kan abubuwan da suka faru kafin kafa jam’iyyar
  • Morka ya bayyana cewa matsalar ita ce lokacin da kamun kafa domin samun muƙami ya koma biyan kuɗi ga masu tasiri domin su taimaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa wasu ministoci na biyan biliyoyin naira domin samun muƙamai a gwamnati.

APC ta bayyana cewa kalaman kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓenta, Alwan Hassan, sun shafi abubuwan da suka faru a baya ne, ba gwamnatin yanzu ba.

APC ta musanta zargin ministoci na biyan kudi
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Sakataren yaɗa labaran APC na kasa, Felix Morka, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Arise Tv a shirin Prime Time.

Kara karanta wannan

An faɗi gwamnatin da ministoci ke biyan biliyoyi domin samun muƙami

Alwan Hassan ya yi wannan zargi ne a wata hira, inda ya ce wasu ministoci kan biya kuɗaɗe masu yawa domin samun naɗi, sannan su fara tunanin yadda za su dawo da kuɗin da suka kashe.

Me APC ta ce kan lamarin?

Da yake mayar da martani kan kalaman, Felix Morka, ya ce Alwan Hassan ya bayyana masa cewa ba gwamnatin Tinubu yake magana a kanta ba, sai dai abubuwan da suka faru a tarihi.

Morka ya ce kalaman Hassan sun bar wasu gurare da za a iya fassara su ta hanyoyi daban-daban.

“Abin da yake magana a kai ba lallai ya shafi wannan gwamnati ba ne, yana magana ne ta mahangar tarihi. Ya bayyana cewa abin da yake magana a kai ya faru kafin kafa APC.” In ji shi.

Morka ya ƙara da cewa wani lokaci masu sharhi kan al’amuran jama’a suna yin magana a dunkule ba tare da fayyace lokacin da suke magana a kai ba.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

Ya ce bai kamata a ɗauki duk wata magana kan matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya a matsayin zargin gwamnatin da ke kan mulki ba.

Sai dai ya jaddada cewa Alwan Hassan ne zai fi dacewa ya yi ƙarin bayani kan ainihin abin da yake nufi.

An tambayi yadda za a mayar da kudin

Morka ya kuma tambayi yadda ministocin da ake zargin sun biya biliyoyin naira domin samun muƙamai za su iya dawo da waɗannan kuɗaɗe bisa tsarin kasafin kuɗin Najeriya.

Ya ce da kansa yana da shakku kan yiwuwar hakan, yana mai cewa ba abu ne da yake son ya yi zato a kai ba.

Ya kuma yi nuni da cewa a wasu ƙasashen dimokuraɗiyya, musamman Amurka, ana amfani da kamfanoni wajen neman goyon baya ga mutane domin a naɗa su muƙaman gwamnati.

Sai dai Morka ya bambanta irin wannan neman goyon baya da tsarin biyan kuɗi ga masu iko ko tasiri domin su samar wa mutum muƙami.

APC ta musanta zargin biyan biliyoyi
Farfesa Nentawe Yilwatda, shugaban jam'iyyar APC na kasa Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Ana so kotu ta soke dan takarar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PRP ta roƙi kotu ta haramta wa APC shiga zaɓen gwamnan jihar Rivers na ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Karar mai lamba FHC/PH/CS/193/2026 ta kuma nemi kotun ta umarci hukumar INEC da ta cire APC da ɗan takararta daga jerin jam’iyyun siyasa da suka cancanci tsayar da ’yan takara a Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng