Atiku Ya Zargi Tinubu da Shirin Tafiya Faransa amma Ya Fake da Zuwa Saudi

Atiku Ya Zargi Tinubu da Shirin Tafiya Faransa amma Ya Fake da Zuwa Saudi

  • Atiku Abubakar ya zargi Bola Tinubu da yiwuwar amfani da tafiyar Umrah a da wata manufa yana mai cewa bayanan sirri sun nuna cewa Faransa ya ke son zuwa
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bukaci fadar shugaban ƙasa ta rika fitar da hotuna da bidiyoyi masu dauke da ranar da aka ɗauke su, domin tabbatar da Tinubu yana Makkah
  • Atiku ya kuma nemi a bayyana cikakken jadawalin tafiyar shugaban ƙasar da yadda ake biyan kuɗin jirgi, tare da amsa tambayoyin da suka shafi lafiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya rika fitar da hotuna da bidiyoyi a kullum domin tabbatar da cewa yana Makkah yana gudanar da ibadar Umrah.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu zai tafi Makkah domin yi wa Najeriya addu’a

Hakan na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana shakku kan ainihin inda shugaban ƙasar zai je.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Atiku ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na dabarun yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu ya fitar.

Zargin da Atiku ya yi wa Tinubu

A cikin sanarwar, Atiku ya ce akwai dalilin zargin cewa Tinubu na iya yin ɗan gajeren zama a Makkah kafin ya wuce zuwa Faransa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi ikirarin cewa bayanan sirri masu inganci da yake da su sun nuna cewa Faransa ce ainihin inda shugaban ƙasar zai je, duk da sanarwar tafiyarsa Umrah.

Atiku ya kuma yi tambayoyi kan ko tafiyar tana da alaƙa da lafiyar shugaban ƙasar da kuma wani rahoton neman rancen dala biliyan 20 da ya shafi wani abokin hulɗar kasuwanci na Faransa.

Batun hotuna da bidiyon Tinubu

Atiku ya ce idan da gaske Tinubu ya tafi Umrah ne domin yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya da ci gaba, ya kamata fadar shugaban ƙasa ta rika wallafa hotuna da bidiyoyi na yanzu, masu ɗauke da ranakun da aka ɗauke su.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Ya bukaci a rika nuna shugaban ƙasar a kusa da Ka’aba da kuma lokacin da yake gudanar da ibadar Umrah.

A cewarsa, ’yan Najeriya na da haƙƙin samun sahihiyar hujjar kasancewar shugaban ƙasar a Makkah da kuma sanin abubuwan da yake yi a kowace rana yayin da yake can.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya ce shi da sauran ’yan Najeriya za su haɗa kai da Tinubu wajen yin salla da addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

ADC ta daga ranar fara kamfen

A wani labari, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta ɗage ranar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasarta a jihar Sokoto daga Asabar, 31 ga Oktoba, zuwa Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne saboda wasu buƙatu da suka shafi shiri da tsara yadda za a gudanar da taron.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa ba za a gudanar da taron a ranar Asabar ba, amma ya ce ana buƙatar tabbatar da sabuwar ranar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng