An Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam'iyyar ADC

An Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam'iyyar ADC

  • Ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADC, Ibrahim Ali Amin da aka fi sani da Little, ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 18 gabanin zaɓen 2027
  • Aminu Labaran Baba ne aka naɗa shugaban kwamitin, yayin da Bala Yau Bayco zai zama darakta-janar na kwamin kamfenn ADC a Kano
  • Adnan Mukhtar ne aka naɗa daraktan yaɗa labarai da sadarwa, yayin da Nasiru Hussaini Agalawa zai kula da harkokin kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar ADC, Ibrahim Ali Amin wanda aka fi sani da Little, ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 18 gabanin babban zaɓen 2027.

A cewar wata sanarwa da Adnan Mukhtar TudunWada, daraktan yaɗa labarai da sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar, ya fitar, ana sa ran kwamitin zai tsara tare da kula da dukkan ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya sha kaye a ƙokarinsa na samun tikitin takarar gwamnan Kano a 2027

Ibrahim Ali Amin Little.
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar ADC, Hon. Ibrahim Ali Amin Little Hoto: Hon. Ibrahim Ali Amin Little
Source: Facebook

Adnan ya wallafa wannan sanarwa mai dauke da sunayen mambobin kwamitin kamfen a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, 2026

Shugabannin kwamitin kamfen ADC

A cikin naɗe-naɗen, an naɗa Hon. Aminu Labaran Baba a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Hon. Bala Yau Bayco zai riƙe muƙamin darakta-janar. An kuma naɗa Yusuf Mamman Bature a matsayin sakatare.

Sauran muhimman naɗe-naɗen sun haɗa da Hon. Mamina Bako Lamido a matsayin daraktan tuntuba, tare da Hon. Abdullahi Dalhatu Dan Kano a matsayin mataimakinsa.

An naɗa Hon. Nasir Tahir daraktan ƙungiyoyin goyon baya, yayin da Aliyu Ibrahim Muhammad zai zama mataimakinsa.

Adnan Mukhtar ne aka naɗa daraktan yaɗa labarai da sadarwa, yayin da Nasiru Hussaini Agalawa zai kula da harkokin kuɗi.

Sauran naɗe-naɗen kwamitin

Haka kuma, ɗan takarar ya naɗa Magaji Yau Indabawa a matsayin daraktan hulɗa da jama’a, Abba Abdulhadi Kofar Waika a matsayin daraktan wayar da kan matasa, sannan Naja’atu Tasiu Abbas ta zama mataimakiyar daraktar.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Haka zalika, an naɗa Sharu Garba Umar Gwammaja a matsayin daraktan ayyuka na musamman, yayin da Aisha Ibrahim Hassan wadda aka fi sani da Humaira za ta jagoranci sashen wayar da kan mata.

Adnan.
Daraktan yada labarai da sadarwa na kwamitin kamfen ADC, Adnan Mukhtar TudunWada Hoto: Adnan Mukhtar TudunWada
Source: Facebook

An naɗa Zahra Ibrahim Aminu a matsayin mataimakiyar daraktar wayar da kan mata. Haka kuma, Aisha Ibrahim Captain, Binta Sayyada da Amina Mahmud za su zama mataimaka masu kula da Kano ta Kudu, Kano ta Tsakiya da Kano ta Arewa bi da bi.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a sanar da ƙarin mambobin kwamitin kamfen dan takarar gwamnan da sauran naɗe-naɗe nan gaba.

Kotu ta yanke hukunci kan tikitin ADC

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban Majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi rashin nasara a karar da ya shigar kotu.

Mai shari’a SM Shuaibu ya yi watsi da ƙarar da malamin ya shigar, inda yake neman a maye gurbin Ali Amin da shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262