Tsohon Ɗan Majalisa Ya Sake Lashe Zaben Fitar da Gwanin APC da Kotu Ta Rusa

Tsohon Ɗan Majalisa Ya Sake Lashe Zaben Fitar da Gwanin APC da Kotu Ta Rusa

  • Tsohon dan majalisar wakilai ya lashe zaben fitar da gwani na APC a mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas da ke Plateau
  • Dan siyasar ya samu kuri’u 12,181, yayin da babbar abokiyar hamayyarsa, Esther Simi Dusu, ta samu kuri’u 2,495 a zaben
  • An gudanar da zaben ne bisa umarnin kotu bayan ta soke zaben farko saboda zargin kura-kurai a rumfunan zabe 11

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Tsohon dan majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.

An gudanar da zaben ne a mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas ta tarayya da ke jihar Plateau a Arewacin Najeriya.

Tsohon ɗan majalisa ya samu tikitin takara
Hon. Dachung Bagos da ya lashe zaben fitar da gwanin APC. Hoto: Dachung Bagos.
Source: Facebook

Bagos ya doke Esther Simi Dusu a zaben da aka gudanar a mazabu 11 a ranar Laraba, bayan samun umarnin kotu, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Babbar kotun da ke Jos ta soke zaben fitar da gwani na farko saboda zargin kura-kurai a mazabu 11, wadanda suka hada da Du, Shen, Zawan ‘B’, Turu, Fobur ‘A’, Fobur ‘B’, Jarawan Kogi, Maijuju/Doss, Federe, Shere ta Gabas da Shere ta Yamma.

Da yake sanar da sakamakon zaben a ranar Alhamis a sakatariyar APC ta jihar, Kalwa House da ke Jos, shugaban kwamitin gudanar da zaben, Simon Elisha, ya ce Bagos ya samu kuri’u 12,181.

Ya bayyana cewa Esther Simi Dusu, wadda ta zo ta biyu, ta samu kuri’u 2,495, lamarin da ya ba Bagos damar lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Elisha ya ce an gudanar da zaben bisa umarnin kotu da kuma ka’idojin jam’iyyar domin tabbatar da gaskiya da adalci.

“An gudanar da zaben bisa umarnin kotu kuma daidai da ka’idojin jam’iyyar domin tabbatar da gaskiya da adalci."

- in ji Elisha.

Da wannan nasara, Bagos, wanda ya taba wakiltar mazabar a Majalisar Wakilai, zai wakilci APC a zaben kujerar dan majalisar wakilai ta Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a babban zaben shekarar 2027.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.