Matasa Sun Kira Sarki a Waya, Sun Yi Barazanar Yin Garkuwa da Shi a Kano

Matasa Sun Kira Sarki a Waya, Sun Yi Barazanar Yin Garkuwa da Shi a Kano

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta kama mutum biyu da ake zargi da yi wa shugaban ƙauyen Bangare barazanar sace shi ta wayar tarho
  • Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ya ce an kama Aliyu Naziru Garba da Bashir Alhasan, dukkansu masu shekaru 20, bayan bincike
  • ’Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin, yayin da bincike ke ci gaba kafin gurfanar da su a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano – Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta dakile wani yunƙurin sace shugaban ƙauyen Bangare da ke ƙaramar hukumar Gezawa.

Rundunar ta kama mutum biyu da ake zargi da haɗa baki wajen aikata laifi da kuma yi masa barazanar aikata laifi.

An kama matasa kan barazanar sace sarki
Kakakin yan sanda a Kano, Abdulahi Haruna Kiyawa. Hoto: Abdulahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan wani matashi da ya yi barazanar sakin hotunan tsiraicin Gwamna Abba

A cewar sanarwar, shugaban ƙauyen Bangare, Malam Idris, ne ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Gezawa ranar 26 ga Oktoba, 2026.

Sanarwar ta ce Malam Idris ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 9:33 na daren ranar 24 ga Oktoba, wani mutum da bai san ko wanene ba ya kira shi ta waya, yana yi masa barazanar sace shi.

Yadda ’Yan Sanda Suka Kama Waɗanda Ake Zargi

Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda na sashen Gezawa sun fara gudanar da bincike cikin gaggawa.

Ta ce haɗa bayanan sirri da ci gaba da bibiyar lamarin ya taimaka wajen kama waɗanda ake zargi guda biyu, wato Aliyu Naziru Garba mai shekaru 20 da Bashir Alhasan, shi ma mai shekaru 20.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, amma ba ta bayyana ƙarin bayanai kan yadda aka shirya barazanar ko ko akwai wasu mutane da ake nema ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, bayan kammalawa kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Yaba da Aikin Jami’ai

Kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da yadda jami’an sashen Gezawa suka gaggauta ɗaukar mataki tare da gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa.

Ya kuma jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in aikata laifuka ba.

Rundunar ta buƙaci al’umma da su kasance masu lura da tsaro, tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suka ga yana da shakku zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Haka kuma, ta bayar da lambobin waya da jama’a za su iya kira domin neman agajin gaggawa: 08032419754, 08123821575 da 09029292926.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.