Kisan Malaman Addini: Daga Sheikh Ja’afar zuwa Yahaya Masussuka

Kisan Malaman Addini: Daga Sheikh Ja’afar zuwa Yahaya Masussuka

  • Kisan Malam Yahaya Masussuka a Katsina ya sake tayar da hankalin jama’a, musamman ganin yadda wasu fitattun malaman addinin Musulunci suka rasa rayukansu a hare-hare a baya
  • A shekarar 2007, an kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a Kano lokacin da yake limancin sallar Asuba, yayin da aka kashe Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani a Zariya a shekarar 2014
  • A wannan karon, kungiyar 'yan ta'adda ta ungiyar Ansaru ta ɗauki alhakin kashe Masussuka, tana zarginsa da kafirci, amma ba ta gabatar da takamaiman hujjar da ta tabbatar da zargin nata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Kisan Malam Yahaya Masussuka, wanda aka harbe a gidansa da ke Dutsin-Ma a Katsina a ranar 26 ga Oktoba, 2026, ta sake dawo da tunanin wasu hare-haren da suka yi sanadin mutuwar fitattun malaman addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Masussuka: Shehu Sani ya faɗi 'dalilai' da ke jawo kisan malamai a Arewa

A cikin shekaru 19 da suka gabata, an kashe malamai da dama a yanayi daban-daban, ciki har da Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya.

Sheikh Albani Zariya, Sheikh Jafar Mahmud Adam da Sheikh Yahaya Masussuka
Wasu malaman da aka kashe a Arewa. Hoto: Muhammad Ahmad|Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku jerin fitattun malaman addinin Musulunci da aka kashe su a Arewacin Najeriya a jiya da yau.

An kashe Sheikh Ja’afar a Kano

A zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, an kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, a ranar 13 ga Afrilu, 2007, a birnin Kano.

An harbe malamin ne yayin da yake limancin sallar Asuba, lamarin da ya girgiza al’ummar Musulmi a Najeriya.

Kisan ya zama ɗaya daga cikin munanan abubuwan da suka faru da fitattun malaman addinin Musulunci a ƙasar, musamman ganin yadda aka kai masa hari a lokacin ibada.

Sheikh Jafar Mahmud Adam
Marigayi Sheikh Jafar da aka kashe a Kano. Hoto: Auwal Adam
Source: UGC

An kashe Albani a Zariya

A ranar 1 ga Fabrairu, 2014, a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, an kashe Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani a birnin Zariya na jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe malamin ne bayan ya kammala salla da kuma karantar da jama’a littafin Hadisi.

Kara karanta wannan

Wadanda suka kashe Sheikh Masussuka sun fito sun bayyana kan su

Kisan Albani ya jawo jimami a tsakanin ɗalibansa da sauran al’ummar Musulmi, musamman ganin yadda ya shahara wajen karantar da ilimin addini.

Marigayi Sheikh Albani Zariya
Sheikh Albani Zariya da makarantar da ya bari. Hoto: Muhammad Hassan
Source: Facebook

An kashe Masussuka a Katsina

A ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, wasu ’yan bindiga sun kashe Sheikh Yahaya Masussuka a ƙofar gidansa da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar malamin. Shugaban ’yan sanda na Dutsin-Ma, CSP Auwalu Gwadabe, ya shaida wa BBC cewa maharan sun harbe malamin a ƙofar gidansa da yammacin ranar.

Sheikh Yahaya Masussuka
Sheikh Yahaya Masussuka da aka kashe a Katsina. Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

Ya ce Masussuka ya rasu ne sakamakon raunukan harbin bindiga bayan an garzaya da shi asibiti.

Sakataren malamin, Dr Mustapha Haruna, shi ma ya tabbatar da rasuwarsa a Babban Asibitin Dutsin-Ma.

Ansaru ta ɗauki alhakin kisan

Bayan kisan, ƙungiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda ta fitar da wani saƙon murya inda ta ɗauki alhakin harin tare da zargin Masussuka da kafirci da adawa da Musulunci.

A cikin saƙon, ƙungiyar ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, duk da cewa mai magana a cikinsa ya ambaci ranar Talata, alhali rahotanni sun nuna cewa an kashe malamin ne a daren Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bazama aiki, sun dauki matakin gano makasan Sheikh Masussuka

Ƙungiyar ba ta bayyana takamaiman laifin da ta ce malamin ya aikata ba.

Sheikh Masussuka da Dikko Radda
Gwamna Dikko Radda tare da Sheikh Masussuka. Hoto: Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Masu daga cikin malaman da aka kashe sun hada da Sheikh Dan Mai Shiyya a Sokoto, Sheikh Albani Gombe, duk da cewa ba su shahara sosai ba.

Gwamnan Katsina ya yi magana

A wani rahoton, kun ci cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi Allah-wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka, yana mai bayyana shi a matsayin mai fafutukar zaman lafiya.

Gwamnan ya buƙaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Mohammed, ya fitar, Radda ya bayyana cewa lamarin ya ba shi mamaki, yana mai jaddada cewa dole ne a hukunta waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng