Yanzu Yanzu: An ratsar da Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo

Yanzu Yanzu: An ratsar da Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an rantsar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo.

Shugaban alkalan jihar, Justis Pascal Nnadi ne ya rantsar da zababben gwamnan da mataimakinsa, Farfesa Placid Njoku.

An gudanar da bikin rantsarwar a gidan gwamnatin jihar Imo, yan sa’o’i bayan Sanata Uzodinma ya amshi takardar shaidar cin zabensa daga hannun hukumar INEC a Abuja.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan kotun koli ta soke zabeb Emeka Ihedioha da kuma kaddamar da Uzodinma a matsayin zababben Gwamnan jihar.

Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar, Sanata Rochas Okorocha da kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APGA a zaben 2019, Ifeanyi Ararume na daga cikin wadanda suka halarci taron rantsarwar.

Rev. Father Ejike Mbaka, wanda ya yi hasashen cewa Sanata Uzodinma zai zama Gwamnan jihar na daga cikin mutanen da suka halarci taron.

KU KARANTA KUMA: Matasan Yobe sun hau dokin naki kan zabar Bulama a matsayin sakataren APC na kasa

Sauran jiga-jigab APC da suka hallara sun hada da mataimakin Shugaban APC na kasa, Emma Enuekwu, sakataren shiryawa na APC, Emma Ibediro, kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Chiji da kuma Ahmed Gulak da Andy Uba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel