Amaechi: An Taso Abokin Takarar Atiku a Gaba kan Zaben 2027

Amaechi: An Taso Abokin Takarar Atiku a Gaba kan Zaben 2027

  • Magnus Abe ya bukaci Rotimi Amaechi ya yi murabus daga tikitin mataimakin shugaban kasa na ADC
  • Abe ya bayyana goyon bayan kungiyar Rainbow Coalition ga sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.
  • Sanatan ya zargi Amaechi da sauya matsayarsa kan tsarin karba-karban shugabanci tsakanin Arewa da Kudu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Sanata Magnus Abe ya bukaci tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, da ya yi murabus daga matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a tikitin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Abe ya ce ya kamata shugabancin Najeriya ya ci gaba da kasancewa a Kudu a zaben 2027, bisa tsarin karba-karban mulki tsakanin Arewa da Kudu.

An bukaci Amaechi ya hakura da takara
Atiku Abubakar, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakon fatan alheri a wani taron kungiyar Rainbow Coalition a Jihar Rivers, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gano abin da ya haddasa rashin tsaro, ya samo hanyar magance matsalar

Ya kuma sanar da goyon bayan kungiyar ga kokarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zabe.

Abe ya zargi Amaechi da sauya matsaya

Abe ya zargi Amaechi da yin watsi da matsayar da ya taba rike wa kan tsarin rabon shugabanci tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya.

Ya tuna cewa a lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya fito daga Kudu maso Kudu, Amaechi ya yi adawa da ci gaba da mulkinsa.

A cewar Abe, a wancan lokacin Amaechi ya yi ikirarin cewa sake wa Jonathan wa’adi zai saba wa yarjejeniyar da ba a rubuta ba, wadda ta tanadi karba-karban shugabanci tsakanin Arewa da Kudu.

Sai dai Abe ya ce yanzu Amaechi yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa daga Arewa, a lokacin da yake ganin ya kamata shugabancin ya kasance a hannun Kudu.

“A yau, mutumin da ya jagorance mu muka yi adawa da dan’uwanmu kuma dan yankinmu, yanzu yana kokarin jagorantar mu mu goyi bayan wani daga Arewa, alhali lokacin Kudu ne.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fusata kan kisan Sheikh Masussuka, sun aika sako ga gwamnati

Ya bukaci Amaechi ya janye daga tikitin Atiku

Sanata Abe ya bukaci Amaechi da ya tsaya kan matsayar da ya taba bayyana a baya ta hanyar janyewa daga tikitin takarar Atiku.

Ya ce a madadin wadanda suka halarci taron a Jihar Rivers, suna kira ga tsohon gwamnan da ya mutunta matsayarsa ta baya.

"Muna kira ga Amaechi da ya gaggauta mutunta matsayarsa, ya yi murabus daga matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku Abubakar.” In ji shi.

Rainbow Coalition ta goyi bayan Tinubu

A yayin taron, Abe ya bayyana cikakken goyon bayan kungiyar Rainbow Coalition ga Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Ya jaddada matsayar kungiyar da kalaman da ke nuna cewa sun hada kai da shugaban kasar, suna mara masa baya kuma za su tsaya tare da shi.

Abe ya kuma ce Jihar Rivers za ta tsaya kan tsarin karba-karban shugabanci tsakanin Arewa da Kudu.

Ya kara da cewa Atiku ya kamata ya mutunta wannan tsarin, duk da cewa a baya ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa kuma ya sha tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bazama aiki, sun dauki matakin gano makasan Sheikh Masussuka

An bukaci Amaechi ya hakura da takara
Atiku Abubakar tare da Rotimi Amaechi Hoto: @atiku
Source: Facebook

Wike ya yi maganar Amaechi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya sake caccakar tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.

Ministan na Abuja ya bayyana cewa Amaechi ba zai taba zama shugaban Najeriya ba inda ya ce zai hana shi kamfen a Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng