Peter Obi Ya Gano Abin da Ya Haddasa Rashin Tsaro, Ya Samo Hanyar Magance Matsalar

Peter Obi Ya Gano Abin da Ya Haddasa Rashin Tsaro, Ya Samo Hanyar Magance Matsalar

  • Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya yi magana kan yawaitar satar mutane da ayyukan ’yan bindiga
  • Obi ya yi alkawarin bin masu garkuwa da mutane har cikin daji tare da daukar tsauraran matakai idan aka zabe shi a 2027
  • Ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa wuraren tarihi da yawon bude ido a Kogi da Plateau domin samar da ayyukan yi da karin kudaden shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro.

Peter Obi ya danganta yawaitar rashin tsaro a Najeriya da matsanancin talauci, inda ya yi alkawarin yaki da fatara domin rage aikata laifuffuka idan aka zabe shi a 2027.

Peter Obi ya yi magana kan rashin tsaro
Peter Obi na jawabi a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Obi ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna

Ya ce yunwa da rashin tsaro sun addabi ’yan Najeriya, lamarin da ya sa wasu mutane shiga ayyukan satar mutane da ta’addancin ’yan bindiga a matsayin hanyar tsira daga mawuyacin hali.

Wane alkawari Peter Obi ya yi?

Dan takarar ya ce gwamnatin NDC za ta mayar da yaki da talauci cikin manyan abubuwan da za ta sa a gaba domin rage aikata laifuffuka a fadin kasar.

Ya bayyana cewa idan aka sace mutum aka kai shi cikin daji, gwamnatinsa ba za ta tsaya a ofisoshin Abuja tana bayar da umarni kawai ba.

Obi ya ce jami’an gwamnati za su bi masu garkuwa har inda suke domin tunkarar matsalar, tare da daukar tsauraran matakai.

Ya kara da cewa ba zai gudu ko ya guji daukar mataki ba idan aka samu matsala a kasar.

“Gwamnatin NDC za ta yaki talauci domin rage aikata laifuffuka. Idan kuka yi garkuwa da mutum kuka kai shi daji, za mu biyo ku har cikin dajin.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi barazanar fitar da hotunan tsiraicin Gwamna Abba

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta rage tsadar rayuwa domin samar da damar da kowane dan Najeriya zai iya samun ci gaba ba tare da sai yana da sanayya da masu fada a ji ba.

Ya zargi wasu jami’an gwamnati

Obi ya ce matsalar rashin tsaro ta kara tayar da hankali saboda wasu jami’an gwamnati da aka damka wa amanar shugabanci suna aikata almundahana da rashawa.

A cewarsa, irin wadannan ayyuka na jawo karkatar da kudaden jama’a zuwa amfanin wasu mutane maimakon a yi amfani da su wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya nuna cewa rage talauci da tsadar rayuwa na iya taimakawa wajen magance wasu matsalolin zamantakewa da ke jefa mutane cikin aikata laifuffuka.

Obi ya yi alkawari kan Kogi

Obi ya bayyana cewa Jihar Kogi na da muhimmanci ta fuskar tarihi, tun daga zamanin kafin mulkin mallaka har zuwa lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye Najeriya.

Ya ce gwamnatin NDC za ta farfado da wuraren tarihi na jihar domin jawo masu yawon bude ido daga kasashen waje, samar da ayyukan yi da kuma kara kudaden shiga ga mazauna yankin.

Ya kuma bayyana cewa albarkatun kasa da wuraren yawon bude ido da ke Kogi da Plateau sun isa su jawo shugabanni da sauran masu ziyara daga cikin Najeriya da wajen kasar domin gudanar da hutunsu a gida.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kashim Shettima ya dura kan Peter Obi, ya yi masa wankin babban bargo

Obi ya yi maganar rashin tsaro
Peter Obi na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Shettima ya soki Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi.

Kashim Shettima ya bayyana cewa babu wani abu na musamman da zai iya gabatar wa ’yan Najeriya baya ga ambaton alkaluman tattalin arzik Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng