Tsohuwar Gaba Ta Yi Kamari: Wike Ya Yi wa Amaechi Mummunan Baki a Siyasa

Tsohuwar Gaba Ta Yi Kamari: Wike Ya Yi wa Amaechi Mummunan Baki a Siyasa

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi yayin da zabe ke kara kusantowa
  • Wike ya yi barazanar cewa za su hana Amaechi kamfen a Rivers idan ya ci gaba da cin mutuncin masu goyon bayan Bola Tinubu
  • Ministan ya zargi Amaechi da almundahana da kuɗaɗen jama’a, inda ya ambaci ayyukan asibiti, layin dogo da wutar lantarki daga ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya sake caccakar tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.

Wike ya bayyana cewa Amaechi ba zai taba zama shugaban Najeriya ba inda ya ce zai hana shi kamfen a Rivers.

Wike ya yi wa Amaechi mummunan fata
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Rotimi Amaechi. Hoto: Lere Olayinka, Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Facebook

Wike ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma’a, bayan ganawa da shugabannin ƙananan hukumomin birnin Abuja, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Amaechi zai iya samu kan shi a matsala saboda kalaman da ya yi game da APC

Wike ya yi martani ga kalaman Amaechi

Ya fadi haka yayin da yake mayar da martani kan kalaman da ake dangantawa da Amaechi, inda ya ce “barayi da mahaukata ne kawai za su zaɓi Shugaba Bola Tinubu.”

Ministan ya bayyana kalaman tsohon gwamnan a matsayin cin mutunci ga magoya bayan shugaban ƙasar, sannan ya ƙalubalance shi da ya yi bayani kan ayyukan raya ƙasa da kuɗaɗen jama’a da ake zargin an yi almundahana da su a lokacin mulkinsa na jihar Rivers.

Wike ya kuma nuna shakku kan cancantar Amaechi na zama shugaban ƙasa, tare da zargin kafafen yaɗa labarai da Hukumar INEC da barin ’yan siyasa su yi amfani da kalaman kamfen da ya bayyana a matsayin waɗanda ba su dace ba.

Ministan ya yi gargaɗin cewa Amaechi zai fuskanci turjiya idan ya yi ƙoƙarin gudanar da kamfen a jihar Rivers yayin da yake ci gaba da cin mutuncin magoya bayan Tinubu.

Kara karanta wannan

Wani talaka ya yi karfin hali, ya ci bashin miliyoyi don yi wa Tinubu kamfen

Ya ce:

“Idan ya ci gaba da wannan hali, zai yi masa wuya ya gudanar da kamfen a jihar Rivers. Za mu ba shii wahala.
“Ba za ka zauna kana kiran masu zaɓe mahaukata da barayi ba, sannan ka yi tsammanin za ka tsallake haka ba tare da fuskantar sakamako ba.”
Wike ya sake caccakar Amaechi
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin jawabi a Rivers. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Wike ya kalubalanci Amaechi kan zargin badakala

Wike ya kuma ƙalubalanci ’yan jarida da su nemi Amaechi ya yi bayani kan ayyuka da kuma mu’amalolin kuɗi daban-daban da aka gudanar a lokacin da yake gwamnan jihar Rivers.

Ministan ya kuma yi tambayoyi kan kwangilar fumigeshan ta dala miliyan 10 da aka bayar ga wani kamfanin Cuba domin yaƙi da sauro, yana mai bayyana aikin a matsayin almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.

Ya lissafa aikin layin dogo na Port Harcourt wanda ya lashe naira biliyan 68, amma aka yi watsi da shi, cikin ayyukan da ya ce suna bukatar a yi tambayoyi kan yadda Amaechi ya gudanar da mulkinsa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Tunanin Tinubu ya mamaye zuciyar minista, yana zuwa har a cikin barci

Wike ya kuma dawo kan batun sayar da kadarorin samar da wutar lantarki ta injinan gas na jihar Rivers, inda ya yi zargin cewa ba a yi cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da dala miliyan 308 da aka samu daga cinikin ba.

Abin da zai sa na yi murabus - Wike

A baya, mun ba ku labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai saka shi ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya ce zai sanar da murabus dinsa ranar 17 ga Janairun 2027, idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers ba a zaɓen shugaban ƙasa.

Ministan ya bayyana cewa yana jagorantar haɗin gwiwar jam’iyyu a Abuja domin samun nasara, tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.