Matasan Arewa Sun Fusata kan Kisan Sheikh Masussuka, Sun Aika Sako ga Gwamnati
- Kungiyar NYCN ta bukaci gwamnatin tarayya da ta Katsina su tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan kisan Sheikh Yahya Masusuka
- An kashe malamin addinin Musulunci da abokinsa, Adamu Abubakar, a harin da wasu ’yan bindiga suka kai a gaban gidan malamin da ke Dutsin-Ma
- NYCN ta ce bai kamata a hukunta waɗanda suka kai harin kai tsaye kawai ba, tana mai bukatar a binciki duk wanda aka samu hujjar cewa ya shirya ko ya dauki nauyin aikata laifin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Kungiyar Northern Youth Council of Nigeria (NYCN) ta yi magana kan kisan da aka yi wa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka.
Kungiyar NYCN ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Katsina su gudanar da cikakken bincike kan kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masusuka, tare da hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Source: Facebook
Shugaban majalisar, Comrade Isah Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026 inda ya yi Allah-wadai da kisan malamin, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Kunguyar ta bayyana kisan a matsayin mummunan hari kan ilimin addinin Musulunci da kuma kyawawan ɗabi'un al'ummar Arewacin Najeriya.
NYCN ta bayyana irin gudummawar malamin
Kungiyar ta bayyana marigayi Sheikh Masusuka a matsayin fitaccen malami kuma mai ba da jagoranci, wanda koyarwarsa ta Alƙur’ani ta yi tasiri ga mutane da dama, musamman matasa a Arewacin Najeriya.
A cewar kungiyar, kisan nasa ya wuce rasa mutum guda, domin yana wakiltar hari kan malaman addini, gaskiya da kyawawan ƙa'idojin da ke taimaka wa zaman lafiya a cikin al'umma.
NYCN ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira ci gaba da faruwar manyan laifufukan kisa ba tare da hukunta waɗanda suka aikata su ba.
Ta ce ya kamata hukumomi su nuna ƙudurin kare rayukan jama'a da tabbatar da cewa duk wanda ya aikata laifi ya fuskanci hukunci.
An bukaci a gudanar da bincike
Kungiyar ta bukaci gudanar da bincike na gaskiya da cikakken bayani domin gano dukkan yanayin da ya kai ga kashe malamin.
Ta ce binciken ya kamata ya duba yiwuwar samun sakaci a ɓangaren tsaro da kuma ko akwai wata babbar maƙarƙashiya, idan hujjoji suka nuna hakan.
Haka kuma, ta bukaci hukumomi su binciki duk wani mutum da za a samu hujjar cewa ya ɗauki nauyin kisan, ya shirya shi ko ya taimaka wajen aiwatar da shi.
A cewar kungiyar, idan bincike ya tabbatar da hannun wasu mutane, bai kamata a tsaya kan kama waɗanda suka kai harin kawai ba.
“Lokacin alkawuran banza, saƙonnin ta'aziyya marasa amfani da kwamitocin bincike na ado ya wuce,” in ji sanarwar.

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya magantu kan kisan Masussuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bukaci al'umma su bar hukumomin tsaro su yi aikinsu kan kisa Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Babban malamin ya bayyana kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a matsayin babban kuskure da ka iya haifar da fitina a cikin al’umma.
Asali: Legit.ng

