'Yan Sanda Sun Bazama Aiki, Sun Dauko Matakin Gano Makasan Sheikh Masussuka
- ’Yan sanda sun fara farautar wasu mutane biyu da ake zargi da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar, a gaban gidan malamin da ke Dutsin-Ma
- Kwamishinan ’yan sandan Katsina, Ali Umar Fage, ya tura jami’an dabaru da na ayyuka yankin domin kamo wadanda ake zargi
- Gwamna Dikko Radda ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya bayyana marigayin a matsayin malamin da ya yi fice wajen wa’azin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta fara farautar wadanda suka kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa Adamu Abubakar a karamar hukumar Dutsin-Ma.
Legit Hausa ta rahoto cewa an kashe mutanen biyu ne a yammacin Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026 a wajen gidan malamin da ke garin Dutsin-Ma.

Source: Facebook
Yadda aka kai hari kan Sheikh Masussuka
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce wasu mutane biyu dauke da makamai, wadanda ke kan babur, sun bude wuta kan malamin da abokinsa a gaban gidan malamin kafin su tsere.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun rahoton harin, jami’in ’yan sanda na sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru.
An garzaya da wadanda aka harba zuwa asibitin da ke kusa domin samun kulawar gaggawa, amma likita ya tabbatar da cewa sun mutu.
Kwamishinan ’yan sanda ya dauki mataki
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an dabaru da na gudanar da ayyuka zuwa yankin domin kamo wadanda ake zargi.
A cewar sanarwar, rundunar ta fara gudanar da bincike tare da kara kaimi wajen gano inda wadanda suka aikata laifin suke da kuma cafke su.
Kwamishinan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokansu, mabiyansu da al’ummar Dutsin-Ma bisa wannan rashi.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an kamo wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Gwamna Radda ya yi Allah-wadai da kisan
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi Allah-wadai da kisan, tare da tabbatar da cewa za a dauki matakan da suka dace domin hukunta wadanda suka aikata shi.
A cikin sakon ta’aziyya da babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, gwamnan ya ce ya girgiza matuka da labarin kisan.
Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar Musulmi da sauran wadanda wannan rashi ya shafa.

Source: Facebook
Amnesty ta yi Allah wadai da kisan Masussuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka.
Amnesty ta jaddada cewa dole ne hukumomi su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe tare da kare rayukan sauran al’umma.
Asali: Legit.ng

