Da Gaske Kudi Aka Bai Wa Yan A4A domin Su Tallata Bola Tinubu a Arewa? An Samu Bayani
- Kungiyar Arewa 4 Asiwaju (A4A) ta musanta zarge-zargen da ake mata ciki har da cewa kudi ta karbo domin tallata Shugaba Tinubu a Arewa
- Wani sakatare a kungiyar, Aliyu Jalal Jalal ya bayyana cewa manufarsu ita ce wayar da kan jama'a domin su sake zaben Tinubu a karo na biyu
- Ya shaidawa Legit Hausa cewa gwamnatin Tinubu na aiki tukuru domin shawo kan kalubalen tsaro da sauran matsalolin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar Arewa 4 Asiwaju (A4A) ta musanta zarge-zargen da ake mata na karbo kwangilar tallata Shigaba Bola Ahmed Tinubu a Arewacin Najeriya kafin zaben 2027.
Daya daga cikin jagororin kungiyar, Aliyu Jalal Jalal ya bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin kara da aka kirkira, yana mai cewa dama sun san za su fuskanci kalubale.

Source: Facebook
Aliyu Jalal, sakataren sashen Academic Community Mobilization Directorate na kungiyar A4A ya yi wa Legit Hausa bayani a wata tattaunawa da wakilinmu ranar Lahadi da ta gabata.
Ya ce manufar A4A shi ne hada kan al'umma a Arewacin Najeriya domin tallafa wa shirin neman wa'adi na biyu na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Dalilin kafa kungiyar Arewa for Asiwaju
Da wakilinmu ya tambaye shi kan manufarsu da kuma shirye-shiryen da suke yi a karkshin tafiyar A4A, Aliyu Jalal ya ce:
"Arewa For Asiwaju wacce aka fi sani da A4A wata babbar kungiya ce ta siyasa da ke haɗa kan al’ummar Arewa domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni, matasa, mata, ƙwararru, malamai, kungiyoyi, da sauran masu ruwa da tsaki a Arewacin Nigeria.
"Wannan kungiya kuma tana aiki tukuru wajen wayar da kan al’umma game da manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin Shugaba Tinubu, musamman waɗanda suka shafi ci gaban Arewa.

Kara karanta wannan
Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu
"Sannan kuma tana ƙoƙarin ƙarfafa ma rawar da matasa, mata, malamai, ɗalibai da sauran ƙungiyoyin al’umma ke takawa wajen tsara makomar siyasa da ci gaban ƙasa.
"Burin Arewa for Asiwaju shi ne gina sahihin goyon baya ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, tare da inganta haɗin kai, ci gaba da kyakkyawar makoma ga Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Shin kudi aka ba yan A4A?
Dangane da zargin kudi aka ba yan Arewa suka dauko tafiyar A4A duk da matsalar tsaro, talauci da sauran kalubalen da yankin ke fuskanta, Aliyu ya maida martani da cewa:
"Eh toh, dama a harkan siyasa dole ne a yi ta cin karo da zargi da korafe korafe daga alumma musamman daga jam'iyun adawa. Amma yawancin wadannan zarge zarge ba gaskiya ba ne.
Ya amince cewe tabbas akwai kalubale na tsaro a Arewa, amma kuma abin tambaya shi ne, mai gwamnati ta ke yi? Yana mai kara wa da cewa ywancin manya manyan shugabannin 'yan ta'adda an kashe su.

Source: Facebook
Aliyu Jalal ya ce yan ta'addan da suka rage tsiraru ne kawai kuma hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin ganin an gama da su.

Kara karanta wannan
A lokacin da ake rokon talaka ya kara hakuri, an saya wa matasan APC motocin 'N1bn'
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu na iya kokarinta wajen ganin ta yi maganin matsalar tsaro a Najeriya.
'Yan Najeriya na kaunar Tinubu'
Kun ji cewa Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce ’yan Najeriya na son Tinubu, yana mai kira gare su su yi watsi da labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
Idris ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin APC a Kaduna a matsayin alamar goyon bayan Tinubu da manufofinsa.
Asali: Legit.ng
