APC Ta Koma Ba Atiku Shawara kan Abin da Ya Kamata Ya Yi wa Tinubu a Zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- APC a Kaduna ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye takararsa ta 2027 tare da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya
- Sakataren yada labaran APC na Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya ce taron maraba da Tinubu a jihar ya nuna cewa shugaban kasar na da goyon baya a Arewa.
- Ya yi watsi da ikirarin cewa an kirkiri wasu bidiyoyin taron da fasahar AI ko kuma an biya mutane domin su halarta, sai dai bai gabatar da hujjoji ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye takararsa ta shugaban kasa a zaben 2027.
Jam'iyyar mai mulki a Najeriya ta bukaci Atiku Abubakar ya hada kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu

Source: Twitter
Sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Hon. Mohammed Sani Haruna, ne ya yi wannan kira yayin wani taron manema labarai a Kaduna, cewar rahoton jaridar Leadership.
Mohammed Sani Haruna ya bayyana taron jama’ar da suka tarbi Tinubu yayin ziyararsa Kaduna a matsayin alamar goyon bayan da shugaban kasar ke samu a yankin Arewa.
Ya ce Atiku ba zai iya dogaro da kuri’un Arewa a matsayin ginshikin burinsa na zama shugaban kasa ba, yana mai cewa yawan mutanen da suka halarci gangamin kaddamar da yakin neman zaben Tinubu ya nuna matsayar yankin.
APC ta tuna wa Atiku alakarsa da Tinubu
Mohammed Sani Haruna ya bukaci Atiku ya marawa Tinubu baya domin, a cewarsa, hakan zai taimaka wajen karfafa hadin kan kasa.
Ya kuma yi ikirarin cewa Tinubu ya taba taimaka wa Atiku wajen samun damar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2011.
“Akwai tarihi da ke nuna cewa Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Atiku Abubakar alheri ta hanyar ba shi wata dama a shekarar 2011 domin ya tsaya takarar shugaban kasar Najeriya.” In ji shi.

Kara karanta wannan
Tinubu na ganin ƴan adawa suka jefa ƙasa a halin ƙunci duk da matakan da ya ɗauka
Ya kara da cewa ya kamata Atiku ya rama wannan alheri ta hanyar goyon bayan Tinubu, maimakon ci gaba da neman shugabancin kasar.
A cewarsa, yanzu ne lokacin da ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna kishin kasa ta hanyar hada kai da shugaban kasa domin moriyar Najeriya.
An yi magana kan shekarun Atiku
Mai magana da yawun APC a Kaduna ya kuma bukaci Atiku, wanda yake gab da cika shekara 80, ya janye daga takarar shugaban kasa.
Haruna ya yi ikirarin cewa ci gaba da neman shugabancin kasar na iya jefa tsohon mataimakin shugaban kasar cikin karin abin kunya.
Ya kuma ce taron Tinubu a Kaduna ya kalubalanci tsammanin ‘yan adawa na samun gagarumin goyon baya daga Arewa, yankin da ake ganin yana cikin muhimman wuraren da Atiku ke sa ran samun kuri’u.

Source: Facebook
An kori dan takara kan tallata Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NDC reshen jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na Majalisar Dokokin jihar, Mohammed Bunu.
Jam'iyyar NDC ta dauki matakin ladabtar ne bisa zargin dan takarar ya shiga tallata Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC.
Asali: Legit.ng