A Lokacin da Ake Rokon Talaka Ya Kara Hakuri, An Saya wa Matasan APC Motocin 'N1bn'
- Shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya yi wa mutanensa rabon sababbin motocin Toyota Prado 2026
- Jam’iyyar NDC ta yi lissafin cewa an kashe sama da N1bn a kan motocin alhali an kyale talakawa suna wayyo Allah
- N1.05bn kiyasi ne da NDC ta yi bisa farashin motocin domin ba a san ainihin kudin da aka kashe a wajen sayensu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar NDC ta soki APC bayan shugaban matasanta na kasa, Dayo Israel, ya sanar da raba sababbin manyan motoci.
Dayo Israel ya yi rabon Toyota Prado na 2026 ga wasu zababbun shugabannin matasa domin taimaka wajen yi wa APC kamfe.

Source: UGC
NDC ta soki kashe N1.05bn kan motocin matasa
NDC ta ce motocin guda bakwai da aka nuna a wani bidiyo sun kai kimanin Naira biliyan 1.015 a cewar jaridar Vanguard.
Jam’iyyar hamayyar ta yi kiyasin cewa kowace mota tana kan Naira miliyan 145 a kasuwa.
NDC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kashe kudi kan jin dadin ’yan siyasa, yayin da talakawa su ke fama.
Tun da Bola Tinubu ya shiga ofis a 2023, kukan tsadar rayuwa ya karu sosai kuma ana ta kokarin kawo a talaka sa'ida a kasar.
NDC ta ce ana tilasta wa ’yan Najeriya su jure wahalhalun sauye-sauyen tattali, amma an ba ‘yan siyasa motoci masu tsada.
Jam'iyyar NDC ta yi kira a guji zaben APC
Saboda haka ne jam’iyyar ta kar yin kira ga ’yan Najeriya da su kada kuri’unsu domin cire APC daga mulki a zaben shekarar 2027.
Ta kuma ce dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi ya kuduri aniyar rage kudin tafiyar da gwamnati idan ya samu nasara.
Meyasa aka raba wa matasan APC motoci?
A nasa bangaren, Dayo Israel ya ce an ba shugabannin matasan APC motocin ne domin taimaka musu wajen harkokin siyasa.
Za a yi amfani da motocin na Prado wajen gudanar da ayyukan wayar da kai da neman goyon bayan masu zabe a fadin Najeriya.
Remi Tinubu ta saya wa 'yan APC motocin?
Dayo Israel ya kuma gode wa uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, bisa goyon bayan da take bai wa tsarin matasan jam’iyyar.
Bayani da hotunan da aka gani ya sa aka fara zargin akwai hannun Sanata Remi Tinubu wajen sayen motocin na biliyoyin kudi.
A doka, Mai dakin shugaba Bola Tinubu ba ta da wani ofis. Sai dai an saba jin ta bada kyautar makudan kudi bayan hawansu mulki.
Matashin ya yi bayanin a kafar sada zumunta na X a ranar Lahadi, 25 ga Oktoba 2026 kamar yadda za a iya gani a shafin Parallel Facts.
2027: Jam'iyyar NDC za ta fara kamfe
Labarin da aka samu shi ne NDC ta kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na 2027 mai mambobi sama da 150.
Jam’iyyar ta naɗa Ibrahim Hussain Abdulkarim a matsayin Darakta Janar a takarar shugaban kasa, zai tunkari APC da ADC.
Seriake Dickson da Babachir Lawal da wasu manyan NDC za su dage wajen ganin nasarar Peter Obi/Rabiu Kwankwaso.
Asali: Legit.ng


