An Yaɗa Zargin Alaƙar Gwamna Bala da APC, Jam'iyyar Ta Feɗe Gaskiya
- Jam’iyyar APC a Bauchi ta musanta rahotannin cewa ta kulla kawance da Gwamna Bala Mohammed da jam’iyyar APM domin cimma muradun siyasa
- APC ta bukaci Gwamna Bala Mohammed ya shiga cikinta a hukumance idan yana son daidaita Bauchi da gwamnatin tarayya domin samun ci gaba
- Sakataren yada labaran APC a Bauchi, Shehu Udubo, ya ce jam’iyyar ba ta san da wata yarjejeniya ba, yana mai nuna shakku kan alakarsa da APM
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC a Bauchi ta musanta rahotannin da ke cewa ta kulla kawancen siyasa da Gwamna Bala Mohammed da jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).
Jam’iyyar ta kuma bukaci gwamnan ya shiga APC a hukumance idan yana son hada kan jihar da gwamnatin tarayya domin samun ci gaba.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, Shehu Udubo, sakataren yada labaran APC a Bauchi, ya ce jam’iyyar ba ta san da wata yarjejeniyar siyasa irin wadda abokan gwamnan ke yadawa ba, cewar Punch.
APC ta shawarci al'umma a Bauchi
Udubo ya bukaci jama’a su yi taka-tsantsan da rahotannin da ke magana kan wannan kawance, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ba ta san da wata yarjejeniya da Mohammed ba a wajen APC.
Ya kuma nuna shakku kan ikirarin kawancen, inda ya yi nuni da yadda Mohammed ke ci gaba da alakantuwa da ’yan takarar APM tare da shiga harkokin yakin neman zabensu, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
A cikin sanarwar, jam’iyyar APC ta Bauchi ta ce tana maraba da yadda Gwamna Bala Mohammed ya yaba da shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sauye-sauyen tattalin arziki da matakan inganta bangaren lafiya.

Kara karanta wannan
Sanata ya tabbatar da abin da ake tsoro a APC, ya ce akwai matsaloli cikin jam’iyyarsu
Jam’iyyar ta kuma bukaci gwamnan da ya dakatar da abin da ta kira tafiyarsa mara nasara a APM, sannan ya koma APC a hukumance.
Sanarwar ta ce:
“Idan da gaske gwamnan yana son hada kan Jihar Bauchi da manufofin ci gaban gwamnatin tarayya, shiga APC zai samar da wata sahihiyar hanya ta hadin kai, daidaito da kuma bunkasa muradun al’ummar Jihar Bauchi.
“Jihar Bauchi tana da matukar muhimmanci, don haka bai kamata ta kasance a gefe ba a babban tsarin siyasar Najeriya.”

Source: Original
APC ta jaddada goyon baya ga Tinubu
Jam’iyyar ta kara da cewa matsayinta ya samo asali ne daga bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jiha da tarayya, jawo karin ayyukan ci gaba, inganta damar samun shirye-shiryen gwamnatin tarayya da kuma bunkasa walwalar al’umma baki daya.
Udubo ya sake jaddada kudurin APC ta Bauchi na goyon bayan ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu, yana mai cewa jam’iyyar tana son jihar ta amfana da manufofi, shirye-shirye da ayyukan raya kasa na gwamnatin tarayya.
Ya kuma bukaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su mayar da hankali kan shugabanci nagari, ci gaba, hadin kai da walwalar al’ummar jihar.

Kara karanta wannan
‘Dan takaran gwamna ya watsa wa NDC kasa a ido da ya fice daga jam’iyya ana cikin kamfe
Gwamna Bala Mohammed ya magantu kan tsaro
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya shaida wa jami'an sojoji cewa za su samu hadin kai domin a shafe yan bindiga da ke damun jama'a.
Ya ce haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzarar rashin tsaro kuma wannan ba zai sa a yi sakaci da rayuka ba.
Gwamnan ya ce ko ɗansa ne ke da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa doka ba, a kama shi, sannan a yi masa hukunci dai-dai da laifin da aka tabbatar.
Asali: Legit.ng
