Yakubu Adamu: Bala Mohammed Ya Tsayar Dan Takarar Gwamna a Bauchi
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya sha alwashin tunkarar duk wani nau’i na magudin zabe a babban zaben 2027
- Bala Mohammed ya yi magana ne yayin da jam’iyyar APM ta tabbatar da shi a matsayin dan takararta na Sanata a mazabar Bauchi ta Kudu
- APM ta kuma ta tabbatar da kwamishinan kudi, Yakubu Adamu, a matsayin dan takararta na gwamna da Nuhu Zaki a matsayin dan takarar Sanata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Jam’iyyar APM ta tabbatar da Dr. Yakubu Adamu a matsayin dan takararta na gwamna a babban zaben 2027 a jihar Bauchi.
Jam’iyyar kuma ta tabbatar da Gwamna Bala Mohammed a matsayin dan takararta na kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan
'Dan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu tikitin takarar gwamna a zaben 2027

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da taron jam'iyyar ne a wani sako da Sanata Bala Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Jam'iyyar APM ta shiryawa 2027
Leadership ta wallafa cewa an gudanar da bikin tabbatar da 'yan takara na jam'iyyar APM a Bauchi a ranar Alhamis a dandalin Sulaiman Adamu da ke fadar gwamnatin jihar.
Shugaban jam’iyyar APM na jihar Bauchi, Auwal Isa, ya ce jam’iyyar a shirye take ta shiga zaben 2027 tare da gabatar da nagartattun ’yan takara don wakiltar ta.
Haka kuma, Hon. Danlami Ahmed Kawule, wanda ya kula da aikin tabbatar da 'yan takarar, ya bayyana cewa APM na samun karfi da karbuwa cikin sauri a fadin jihar Bauchi gabanin zaben 2027.
Bayanin dan takarar gwamnan Bauchi
A cikin jawabin karbar takara, tsohon kwamishinan kudi a jihar Bauchi, Dr. Yakubu Adamu, ya yi alkawarin daurawa kan nasarorin gwamna Bala Mohammed idan aka zabe shi.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnoni 7 da suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a zaben 2027
Ya ce hangen nesa, nasarori da salon shugabancin gwamnan ne suka zaburar da shi shiga takara, tare da kudirin ci gaba da aikin da aka samu cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Dr. Adamu ya yaba wa shugabancin APM, ’yan jam’iyya da magoya baya a fadin jihar bisa amincewa da goyon bayansu, yana mai bayyana tsarin dimokuradiyyar cikin jam’iyya a matsayin babban karfi.

Source: Facebook
Bayanin Gwamna Bala Mohammed
Haka kuma, Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne dan takarar Sanatan Bauchi ta Kudu na APM, ya yaba wa dukkan ’yan takara bisa rawar da suka taka wajen karfafa dimokuradiyya a jam’iyyar.
A bayanin da ya yi, Bala Mohammed ya ce sadaukarwarsu da jajircewarsu sun taimaka wajen ci gaban jam’iyyar sosai.
A cewarsa, shugabanci yana da nasaba da amana, sauke nauyi, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar APM.
An tsayar da dan takara a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da 'yan takara a Kano.
Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa Aminu Abdulsalam Gwarzo ne zai yi wa jam'iyyar NDC takarar gwamna a jihar Kano a 2027.
Bugu da kari, Kwankwaso ya sanar da cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna ne zai yi wa jam'iyyar takarar Sanata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng