APC Ta Gane Tasirin Arewa, Ta Faɗi Ƙarfin Ikon Talakawa, Ƴar Siyasar Yankin

APC Ta Gane Tasirin Arewa, Ta Faɗi Ƙarfin Ikon Talakawa, Ƴar Siyasar Yankin

  • Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana muhimmancin Arewacin Najeriya ga jam'iyyar ana shirin zabe
  • Basiru ya bayyana cewa wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, sun sauya sheƙa domin tallafa wa APC
  • Sakataren APC ya soki ’yan adawa kan rashin amincewa da shan kaye, yana mai cewa dole ’yan siyasa su karɓi nasara da rashin nasara a dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana Arewacin Najeriya a matsayin babbar cibiyar ƙarfin jam’iyyar mai mulki gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya dage cewa manyan ’yan siyasa da talakawa a yankin suna goyon bayan jam’iyyar, yana mai nuna kwarin gwiwar jam'iyyar APC za ta samu nasara a zaɓen.

Kara karanta wannan

"Babu zagi": Yari ya fadi abin da za su tallata Shugaba Tinubu da shi

APC ta fadi tasirin Arewacin Najeriya
Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Basiru ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television ranar Laraba.

An yi hasashen makomar APC a Arewa

Ya ce yana da kwarin gwiwa kan makomar APC a Arewa, inda ya yi nuni da goyon bayan manyan ’yan siyasa da kuma buɗe wani ofishin yaƙin neman zaɓe mai suna Arewa for Asiwaju.

Basiru ya ce:

“Ƙarfin APC yana Arewacin wannan ƙasa, kuma da yardar Allah za ku ga hakan idan zaɓen 2027 ya zo. A ranar Asabar, mun samu manyan mutane a siyasa, tattalin arziki da masana’antu sun taru domin bayar da gudummawar ofishin yaƙin neman zaɓe da suka kira Arewa for Asiwaju.”

Ya ƙara da cewa wasu ’yan siyasa da ke jam’iyyun adawa sun sauya sheƙa, ciki har da tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, waɗanda yanzu suke shigowa domin aiki tare da APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba

Basiru ya ce:

“Wasu ma da suke jam’iyyun adawa sun sauya sheƙa. Mutane kamar tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, yanzu duk suna zuwa domin shiga APC da yin aiki tare da ita.
“Gaskiyar magana ita ce, a yau idan ka kalli manyan mutane a Arewacin Najeriya, suna tare da mu. Haka kuma, talakawan Arewacin Najeriya suna tare da mu.”
An yaba wa Tinubu kan ayyukan alheri
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

APC ta soki jam'iyyun adawa a Najeriya

Sakataren APC na ƙasa ya kuma soki Jam’iyyun Adawa kan yadda suke mayar da martani idan aka kayar da su a zaɓe, yana mai cewa ya kamata su koyi amincewa da shan kaye a matsayin wani ɓangare na tsarin dimokuraɗiyya.

Basiru ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin ’yan siyasa su amince da nasara da rashin nasara, yana mai cewa APC ma ta taɓa shan kaye a kotu da kuma fafatawar siyasa, amma ta ci gaba da tafiya.

Matawalle ya ba yan majalisar Zamfara motoci

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

A baya, an ji cewa karamin ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bai wa ’yan majalisar dokokin Zamfara takwas da suka koma APC motoci.

Yan majalisar sun gode wa Matawalle bisa tallafin, tare da alƙawarin yin aiki tukuru domin marawa Bola Tinubu baya.

Dattawan APC sun yaba wa Tinubu da Matawalle kan sulhunta ’yan jam’iyyar, amma sun buƙaci a magance sauran ƙorafe-ƙorafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.