2027: PDP, NDC Sun Shiga Kafar Wando da INEC kan Cire Sunayen Yan Takararsu

2027: PDP, NDC Sun Shiga Kafar Wando da INEC kan Cire Sunayen Yan Takararsu

  • Jam’iyyun PDP da NDC sun yi barazanar maka INEC a kotu idan hukumar ta gaza saka sunayen ’yan takararsu
  • INEC ta cire sunayen wasu ’yan takara, ciki har da Farfesa Isa Pantami na Gombe da Oladipupo Adebutu na Ogun
  • Jam’iyyun sun ce sun rubuta wa INEC wasiƙu kan cire ’yan takararsu, amma za su dauki dauki mataki idan hukumar ta gaza gyara kuskuren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyun PDP da Nigeria Democratic Congress (NDC) sun yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Sun ce za su dauki mataki ne idan ta gaza saka sunayen ’yan takararsu da aka cire daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027.

NDC, PDP sun yi wa INEC barazana
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Isa Pantami da takwaransa na NDC a Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Mohammed Jungudo, da takwaransa na NDC, Osa Director, sun shaida wa jaridar The Punch a tattaunawa ta musamma.

Kara karanta wannan

Yan takarar gwamnan jam'iyyar adawa sun fadi wanda za su yi a zaben shugaban kasa

Ya ce jam’iyyunsu za su yi la’akari da kai ƙara kotu idan ba a samu sauyi ba kafin ranar 24 ga Oktobar 2026.

Yadda INEC ta fitar da yan takara

Bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan batun rajistar mambobin jam’iyyu da bayanan rajista, INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna na ƙarshe a zaɓen ranar 6 ga Fabrairu, 2027, a ranar 10 ga Oktoba, inda ta cire sunayen wasu ’yan takara.

Jerin sunayen, wanda sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi ’yan takara 13.

Daga cikin fitattun ’yan siyasar da ba a saka sunayensu ba akwai tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Pantami, wanda shi ne ɗan takarar gwamna na PDP a Gombe, da kuma Oladipupo Adebutu, ɗan takarar jam’iyyar a Ogun sai dan takarar gwamnan Kano a ADC, Aminu Gwarzo, tsohon Sanata Danjuma Tella La’ah a Kaduna.

Kara karanta wannan

Manyan yan sanda sun shiga matsala bayan yan kungiyar asiri sun gyara caji ofis

Hukumar ta sanya ranar 24 ga Oktoba, 2026, a matsayin ranar ƙarshe ta gabatar da irin waɗannan sanarwar.

An cire sunan dan takarar gwamnan NDC a Kano
Dan takarar gwamnan NDC a Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Source: Twitter

PDP ta ce za ta iya kai INEC kotu

Da yake mayar da martani, Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa ya ce shugabannin jam’iyyar da lauyoyin ’yan takarar sun tuntubi INEC, amma har yanzu ba a samu wani sauyi ba.

Ya ce:

“Muna ci gaba da tattaunawa da su, amma akwai yiwuwar mu ƙare a kotu. Ya zuwa ranar Juma’ar makon da ya gabata, babu wani sabon ci gaba. Babu wani abin da ya sauya, kuma ba a samu ci gaba ba.
“Duk da haka, idan aka kai ƙarshen lokacin da ƙa’idojin suka tanada, za mu jira kwanaki 14 ɗin su cika domin ganin abin da zai faru. Idan babu wani ci gaba, ba za mu sami wani zaɓi ba illa neman mafita ta hanyar doka.
“Kamar yadda kuke gani, lauyoyin Pantami sun riga sun rubuta wa INEC. Har yanzu muna fatan cewa wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada zai kawo mana sakamako mai kyau. Amma idan hakan bai faru ba, za mu nemi mafita ta hanyar doka."

Kara karanta wannan

Takarar Pantami da hadu da sabon kalubale daga babban dan PDP

NDC ta ce za ta ɗauki matakin doka

Shi ma Sakataren Yaɗa Labaran NDC ya ce jam’iyyar za ta bi hanyoyin doka bayan wa’adin kwanaki 14 ya ƙare, cewar Tribune.

Ya ce:

“Mun rubuta wa hukumar wasiƙu, kuma sun karɓe su tare da tabbatar mana da karɓarsu. Mun sanar da su kamar yadda doka ta tanada, amma har yanzu ba su ba mu amsa ba.
“Amma idan ta gaza gyara cire sunayen ’yan takararmu daga jerin, mu a matsayin jam’iyya mai bin doka, za mu ɗauki sauran matakan da doka ta tanada domin tabbatar da an yi abin da ya dace."

Zaben 2027: An maka INEC a kotu

An ji cewa SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin INEC da rashin yin cikakken bayani kan sama da N126.46bn.

Ƙungiyar ta nemi kotu ta tilasta wa INEC bayyana yadda aka kashe kuɗin, waɗanda suka amfana da su da kuma kamfanonin da suka karɓi kwangiloli.

Rahoton binciken kuɗaɗen gwamnati ya yi zargin an biya N112.15bn kan kayan zaɓe ba tare da bin ƙa’idojin sayen kayayyaki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.