Yan Takarar Gwamnan Jam’iyyar Adawa Sun Fadi Wanda Za Su Yi a Zaben Shugaban Kasa
- Ƙungiyar ’yan takarar gwamnan jam’iyyar DLA ta amince da sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
- ’Yan takarar sun ce ba za su koma APC ba, domin za su ci gaba da neman kujerun siyasa ƙarƙashin jam’iyyarsu ta DLA
- Aboki Bayonga ya ce suna son ci gaba da manufofin Tinubu, yana mai cewa wa’adin shekaru huɗu bai isa kammala dukkan ayyuka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata ƙungiyar ’yan takarar gwamnan jam’iyyar Democratic Leadership Alliance (DLA) ta fitar da matsaya kan zaben shugaban kasa.
Yan takarar daga sassa daban-daban na Najeriya ta amince da Shugaba Bola Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu a shekarar 2027.

Source: Twitter
Tinubu ya kara samu goyon baya a 2027
Ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar gwamnan DLA a Taraba, Hon. Aboki Bayonga, ce ta bayyana wannan matsaya a wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja ranar Juma’a, cewar Punch.
Ta kuma yi alƙawarin amfani da hanyoyin sadarwarta na siyasa a matakin tushe domin tattara goyon bayan jama’a ga sake zaɓen shugaban ƙasar.
’Yan takarar sun kuma bayyana cewa za su haɗa kai da ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) domin samun ƙarin goyon baya ga shugaban ƙasa.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai sakataren ƙungiyar, Alhaji Adamu Idrisu Chado na Kaduna; Hon. Bekky Folorunso James na Osun; Farfesa Valdya Tame na Adamawa; Hon. Ibrahim Musa na Abuja; Hon. Sam Umar na Plateau; Alhaji Sani Mohammed na Gombe; Hon. Nnamdi Ugwu na Enugu da Hon. Brent Micheal na Bauchi, da sauransu.
Sai dai ’yan takarar sun yi watsi da yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda suka fayyace cewa goyon bayansu ga Tinubu ya shafi zaɓen shugaban ƙasa ne kawai.
Sun jaddada cewa za su ci gaba da neman kujerun gwamna, sanata, wakilai a Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dokokin jihohi ƙarƙashin tutar DLA.
Bayonga ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan shawarwari tsakanin ’ya’yan jam’iyyar, waɗanda suka amince su goyi bayan Tinubu saboda DLA ba za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba a zaɓen 2027.
Ya jaddada cewa wannan goyon baya ba yana nufin sun bar jam’iyyarsu ba ne, yana mai cewa za su ci gaba da kasancewa cikin DLA tare da tsayawa takarar kujerunsu a ƙarƙashin jam’iyyar.
Bayonga ya ce:
“A matsayimmu na ƙungiyar ’yan takarar gwamnan DLA, mun zo nan yau domin bayyana goyon bayanmu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararmu na shugaban ƙasa a 2027. Ba wai mun ajiye burinmu na siyasa ƙarƙashin jam’iyyarmu ba ne. Amma game da kujerar shugaban ƙasa, muna tare da Asiwaju dari bisa ɗari.
“Za mu yi aiki domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo kan mulki. Za mu yi duk abin da za mu iya domin tabbatar da dawowar Asiwaju a 2027.
Bayonga ya bayyana cewa shekaru huɗu ba su isa aiwatar da shirye-shiryen da ke buƙatar tsare-tsare na dogon lokaci da kuɗaɗe masu yawa ba. Ya ƙara da cewa wani wa’adin zai ba gwamnati damar kammala ayyukanta da cimma manufofinta.
Ya ce:
“Muna son a ci gaba. Shekaru huɗu ba su isa kammala dukkan shirye-shirye ba, musamman ayyukan da ke buƙatar tsare-tsare na dogon lokaci da kuɗaɗe masu yawa.”
Da aka tambaye shi ko shugaban ƙasa na jam’iyyar DLA da sauran ’yan takarar gwamnan sun amince da wannan matsaya, Bayonga ya ce:
“Eh. Ni ne shugaban ƙungiyar ’yan takarar gwamnan DLA. Kuma kuna iya ganin dukkanmu a nan. Mun amince, kuma mun gudanar da babban taro jiya, inda muka cimma matsayar abin da muke yi a yau.”
Ya bayyana kyakkyawan fata cewa tsarin siyasa da suka gina da kuma alaƙar da suke da ita da masu zaɓe a jihohinsu za su taimaka wajen samun goyon baya ga shugaban ƙasa.
An caccaki Kwankwaso kan zargin aikin Tinubu
A wani labarin, an ji cewa kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da ƙoƙarin taimaka wa.
Shugaba Bola Tinubu Kakakin kwamitin kamfen din ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kiran Kwankwaso ga Atiku a matsayin abin da bai dace ba.
ADC ta ce Atiku na iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Kano ko da Kwankwaso bai mara masa baya ba, tana mai cewa jama'a za su zabe shi.
Asali: Legit.ng



