Tawagar Tinubu Ta Tafi Neman Addu'a Fadar Manyan Sarakuna a Najeriya

Tawagar Tinubu Ta Tafi Neman Addu'a Fadar Manyan Sarakuna a Najeriya

  • Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya ziyarci sarakunan gargajiya na Ibadan da Oyo domin neman albarkarsu gabanin zaɓen 2027
  • Kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Zamfara, Abubakar Yari, ya ce addu’o’in sarakunan gargajiya na da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar sake zaɓen Bola Tinubu
  • A nasa ɓangaren, Tompolo ya bayar da motoci 32 ga ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Oyo domin ƙara ƙarfafa yaɗa manufofin APC a matakin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo – Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na zaben 2027 ya ziyarci Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, da Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade, domin neman albarkarsu.

Kwamitin ya kai ziyarar ne a ranar Alhamis a fadar sarakunan da ke Ibadan da garin Oyo, yayin da yake shirin yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Abdulaziz Yari a jihar Oyo
Tawagar yakin neman zaben Tinubu a Oyo. Hoto: Sunday Dare
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa daraktan janar na kwamitin, Abubakar Yari ya ce sun ziyarci sarakunan ne domin neman addu’o’insu da goyon bayansu wajen gudanar da aikin da aka ɗaura masu.

Kwamitin Tinubu ya nemi addu'a

Da yake jawabi a fadar Olubadan da ke Oke-Aremo, Yari ya ce Shugaba Tinubu ne ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Laraba, kuma ziyarar Ibadan ita ce ta farko da suka fara kaiwa.

Ya ce hakan ya nuna muhimmancin da birnin Ibadan ke da shi a wajen shugabancin jam’iyyar APC.

Yari ya bayyana cewa Tinubu ya umarci kwamitin da ya ziyarci sarakunan gargajiya a faɗin ƙasar nan domin neman goyon bayansu wajen sake zaɓen shugaban ƙasar a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Ya ce:

“Mun dogara da sarakunan gargajiya wajen gudanar da wannan aiki. Ba za mu iya samun nasara ba tare da albarkarsu da addu’o’insu ba.”

Yari ya kuma ce kwamitin zai yi yaƙin neman zaɓe ne bisa nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a cikin shekara uku da suka gabata, tare da bayyana ayyukan da take shirin aiwatarwa idan aka sake zaɓen ta.

Kara karanta wannan

An hura wa Tinubu wuta kan 2027, ana so ya hakura da shiga takara

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ayyukan da gwamnatocin baya suka fara, inda wasu aka kammala wasu kuma ke gudana.

Olubadan ya yabi Tinubu

Da yake mayar da martani, Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, ya gode wa kwamitin bisa girmamawar da ya nuna wa masarautar gargajiya.

Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya wallafa a Facebook cewa ya kuma yaba wa gudunmawar gwamnatin Tinubu wajen bunƙasa tattalin arziki.

APM ta soki Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APM ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya halarci tarukan yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohin Najeriya ko kuma ya janye takararsa ta 2027.

Kiran nasu ya biyo bayan bayanin da Tinubu ya yi a lokacin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ranar Laraba, inda ya ce ba zai halarci wasu tarukan kamfen ba.

A cikin wata sanarwa ranar Alhamis, Daraktan Sadarwa na MDPCO, Richard Ihediwa, ya ce ƙin halartar dukkan jihohin na iya nuna ƙoƙarin kauce wa fushin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng