Ana Zargin Kwankwaso na Taimakon Tinubu Ya Zarce sabdao Wasu Dalilai

Ana Zargin Kwankwaso na Taimakon Tinubu Ya Zarce sabdao Wasu Dalilai

  • Kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da ƙoƙarin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu
  • Kakakin kwamitin kamfen din ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kiran Kwankwaso ga Atiku a matsayin abin da bai dace ba
  • ADC ta ce Atiku na iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Kano ko da Kwankwaso bai mara masa baya ba, tana mai cewa jama'a za su zabe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kwamitin kamfen din ADC ya soki ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, kan kiransa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya janye wa Peter Obi a zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, daraktan yaɗa labarai na kamfen din ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana kalaman da aka danganta ga Kwankwaso a matsayin waɗanda aka yi don biyan muradin kansa.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓen 2027, Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinoni 6 a INEC

Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu
Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Zargin da ADC ta yi wa Kwankwaso

Daily Trust ta wallafa cewa Ologbondiyan ya ce kiran Kwankwaso, wanda ya yi a wata hira, yunƙuri ne na taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kare muradun siyasar sa gabanin zaɓen shugaban ƙasa.

Ya zargi tsohon gwamnan Kano da mayar da hankali kan shugabannin ’yan adawa maimakon sukar gwamnatin Tinubu, wadda ya ce ’yan Najeriya ke son kaɗawa a zaɓe.

A cewarsa, ya kamata Kwankwaso, a matsayinsa na ɗan adawa da ke son ganin an sauya gwamnati, ya mayar da hankali wajen ƙarfafa ’yan adawa maimakon raunana wani shugabansu.

Ologbondiyan ya kuma yi zargin cewa yunƙurin Kwankwaso na iya kasancewa yana da alaƙa da burinsa na siyasa na shekarar 2031.

ADC ta ce Atiku zai lashe Kano

Kakakin kwamitin ADC ya bayyana cewa Atiku zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano, wadda ita ce tushen siyasar Kwankwaso, ko da tsohon gwamnan bai mara masa baya ba.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya jawo wa mawaki Davido matsala da ya goyi bayan Tinubu

Vanguard ta rahoto ya ce matsin tattalin arziki, yunwa, talauci da rashin tsaro da ’yan Najeriya ke fuskanta za su taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar wanda za su zaɓa.

Ologbondiyan ya kuma yi nuni da zaɓen shugaban ƙasa na shekarun 2003 da 2007, inda ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a Kano duk da cewa bai samu goyon bayan Kwankwaso a zaɓukan ba.

Ya yi amfani da misalan wajen ƙalubalantar ra’ayin cewa goyon bayan Kwankwaso shi ne mabuɗin nasarar duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa a Kano.

Me Kwankwaso ya ke so?

Ologbondiyan ya ce kalaman Kwankwaso sun haifar da tambayoyi kan ainihin ɓangaren siyasar da yake son taimakawa a zaɓen 2027.

Ya yi zargin cewa matakan Kwankwaso sun fi amfani ga jam’iyyar APC mai mulki fiye da ƙarfafa ’yan takarar ’yan adawa, yana mai cewa irin wannan dabara na iya haifar da ruɗani da rarrabuwar kai a tsakanin masu neman sauya gwamnati.

Ya kuma ambaci cewa Kwankwaso ya taɓa bayyana matsayin mataimakin shugaban ƙasa a matsayin kamar tayar mota ta ajiya, yana mai cewa hakan na iya nuna cewa hankalinsa ya fi karkata ga shirye-shiryen siyasar 2031.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Atiku Abubakar a gidan shi
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kwankwaso ya ba Obi kariya

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya kare ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsa, Peter Obi.

Ya ba shi kariya ne bayan da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana shi a matsayin wanda ya ƙware wajen bayar da ƙididdiga marasa tushe da shawarwarin tattalin arziki marasa ma’ana.

Kwankwaso ya mayar da martani ga kalaman Shettima ne a ranar Alhamis, inda ya ce bai yi mamakin abin da mataimakin shugaban ƙasar ya faɗa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng