An Hura wa Tinubu Wuta kan 2027, ana So Ya Hakura da Shiga Takara
- Jam'iyyar APM da ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya fuskanci 'yan Najeriya a dukkan jihohi ko kuma ya janye aniyarsa ta sake takara
- A lokacin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Tinubu ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓe ba
- Shugaban ƙasar, wanda ya kafa hujja da cewa ba ya son aikin gwamnati ya samu cikas, ya yi alƙawarin samun lokacin magana da 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam'iyyar APM tare da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Makinde/Daura (MDPCO) sun buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya je kamfen dukkan jihohi ko kuma ya haƙura da neman sake zaɓensa a 2027.
Wannan martani na zuwa ne sakamakon sanarwar da Tinubu ya yi lokacin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na jam'iyyar APC a ranar Laraba, inda ya ce zai guje wa halartar wasu tarukan domin kula da aikin gwamnati.

Kara karanta wannan
Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa mai kula da dabarun sadarwa na MDPCO, Richard Ihediwa ya bayyana matakin shugaban a matsayin yunƙurin guje wa fushin al'umma saboda halin da gwamnatinsa ta jefa ƙasar a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.
Matakin da APM ke buƙata
Ihediwa ya bayyana cewa matakin na gurgunta tsarin dimokuraɗiyya da kuma muzanta wa masu zaɓe, tare da sake tabbatar da fargabar da 'yan Najeriya ke da ita ta cewa shugaban ba shi da ƙarfin gudanar da mulkin ƙasa kamar Najeriya.
Ya bayyana cewa:
"Matakin ƙi zuwa yaƙin neman zaɓe a fadin ƙasar yana sake ƙarfafa fargabar jama'a cewa jam'iyyar APC ba ta shirya gudanar da zaɓe mai adalci da inganci ba, a maimakon haka tana ƙulla dabarun murɗiya."
Taqaddama kan ayyukan gwamnati
Ledership ta rahoto cewa MDPCO ta bayyana cewa idan har shugaban ƙasa yana takama da cewa ya yi aiki mai kyau, ya kamata ya fito fili ya kare ayyukansa a gaban jama'a maimakon neman uzuri.
A cewar kungiyar, cire tallafin fetur ba tare da tsari mai kyau ba da kuma rage darajar naira sun jefa miliyoyin gidaje cikin mawuyacin halin matsin rayuwa da talauci.

Source: Twitter
Dele Momodu ya soki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa jigo a jam'iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa jam'iyyar ta san dabarun da za ta yi amfani da su domin hana Shugaba Bola Tinubu samun nasarar zarcewa a zaɓen 2027.
Momodu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a kan dabarun siyasa, inda ya ce Tinubu ya fuskanci matsaloli a lokacin da yake gwamnan Jihar Legas.
Ya kuma nuna shakka a kan ingancin INEC ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, inda ya yi zargin cewa shugaban ya naɗa mutane da dama daga shiyyar Kudu maso Yamma a cikin hukumar.
Asali: Legit.ng
