'Yan Kwankwasiyya Sun Tafi Ofishin INEC kan Cire Sunan Aminu Gwarzo
- Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci INEC ta yi bayani kan rashin sunan Aminu Abdussalam Gwarzo da Mustapha Rabi’u Kwankwaso a jerin ’yan takarar gwamnan Kano
- Kungiyar ta ce tana da yakinin cewa za a iya warware matsalar ta hanyoyin gudanarwa ko na shari’a, tare da kira ga jam’iyyar NDC ta gaggauta daukar mataki
- Kwankwasiyya ta bukaci magoya bayanta su kwantar da hankalinsu, su guji yada bayanan da ba a tantance ba, su kuma ci gaba da harkokin siyasa cikin lumana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci INEC ta yi karin bayani kan rashin sunan dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa, Mustapha Rabi’u Kwankwaso a jerin 'yan takara.
A cikin wata sanarwa da kakakinta, Dr Habibu Sale Mohammed, ya fitar ranar Lahadi, kungiyar ta ce lamarin ya jawo damuwa a tsakanin magoya bayanta.

Kara karanta wannan
PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa duk da damuwa da suka shiga, Kwankwasiyya ta bukaci jama'ar ta da su guji hasashe da yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Gwarzo ya yi rajista a kan lokaci
Sanarwar ta bayyana cewa, a fahimtar kungiyar, Gwarzo ya yi rajista da jam’iyyar NDC a cikin wa’adin da aka kayyade.
Kungiyar ta ce ba ta da masaniyar wata shari’a ko umarnin kotu da aka ambata a matsayin dalilin cire sunan dan takarar daga jerin.
Saboda haka, ta bukaci INEC ta bayyana dalilin da ya sa sunayen Gwarzo da mataimakinsa ba su bayyana ba, tare da tabbatar da cewa an kula da lamarin yadda ya kamata.
An bukaci NDC ta bi doka
Kwankwasiyya ta bukaci shugabancin NDC da lauyoyin ’yan takarar su duba sashe na 32(2) na Dokar Zabe ta 2026, wanda sanarwar ta ce ya tanadi wa’adin kwanaki 14 domin sanar da INEC bayanan 'yan takara a rubuce.
Ta kuma shawarci jam’iyyar da ta tattara takardun da za su taimaka wajen tabbatar da matsayinta, ciki har da shaidar rajista, tsayar da dan takara, mika bayanansa da kuma takardun tabbatar da karbar wadannan bayanai.
Sai dai kungiyar ta ce ba za ta riga ta yanke hukunci kan matsayin INEC ko sakamakon duk wata shari’a ba, tana mai jaddada muhimmancin sahihan hujjoji da bin tsarin doka.
An gargadi 'yan Kwankwasiyya
Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci magoya bayanta su ci gaba da harkokin siyasa na halal cikin lumana, ba tare da yin arangama da kowa ba.
Ta ce shugabancinta zai ci gaba da sanya ido kan yadda lamarin ke gudana, tare da sanar da jama’a sahihan bayanai yayin da suke samuwa.

Source: Facebook
Kwankwasiyya ta sake kira ga INEC da ta yi bayani kan rashin sunayen ’yan takarar ba tare da bata lokaci ba, sannan ta bukaci NDC ta yi amfani da dukkan hanyoyin da doka ta tanada cikin wa’adin da aka kayyade.
An cire sunan Pantami a Gombe
A wani rahoto mai alaka da jerin sunayen ’yan takarar gwamna da INEC ta fitar, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, bai bayyana a jerin ’yan takarar gwamnan jihar Gombe ba.
INEC ta fitar da jerin sunayen ne bisa alkawarin da shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, ya yi a wani taron manema labarai a Abuja a farkon makon.
Jerin ya nuna cewa an amince da ’yan takara 16 domin fafatawa a zaben gwamnan Gombe da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Asali: Legit.ng

