Shin Tinubu Ya Karya Doka da Ya Ce ba Zai Je Kamfe Wasu Jihohin Najeriya ba? An Samu Bayani

Shin Tinubu Ya Karya Doka da Ya Ce ba Zai Je Kamfe Wasu Jihohin Najeriya ba? An Samu Bayani

  • Wani jigo a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya ce babu dokar da ta wajabta wa ɗan takarar shugaban ƙasa zuwa kamfe a duka jihohi 36
  • Obafemi George ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya, dokar zaɓe da ƙa’idojin APC ba su fayyace yadda ɗan takara zai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe ba
  • Jadawalin yaƙin neman zaɓen APC da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna cewa Tinubu zai halarci gangami a jihohi 12 kacal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigera - Obafemi George, mamba a sashen yaɗa labarai da dabarun sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya yi magana kan matakin Shugaba Bola Tinubu na takaita zuwa kamfe.

Ya ce babu wata doka da ta wajabta wa ɗan takarar shugaban ƙasa ziyartar dukkan jihohi 36 domin gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya yi kira ga majalisa bayan nada sababbin mukamai a INEC

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

George ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake magana a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise, inda yake mayar da martani kan sukar da ake yi wa Shugaba Bola Tinubu.

Matakin da Bola Tinubu ya dauka

A wajen ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zabe ranar Laraba, Tinubu ya ce ba zai halarci dukkan gangamin kamfe ba, yana mai cewa gudanar da mulki shi ne babban abin da ya fi ba da muhimmanci.

Sai dai ya ce zai ware lokaci domin yin magana kai tsaye da ’yan Najeriya, yayin da shugabannin APC za su riƙa zagaya jihohi da ƙananan hukumomi domin neman goyon bayan jama'a

A ranar Alhamis, jadawalin yaƙin neman zaɓen APC da ya bazu a kafafen sada zumunta, ta nuna cewa Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi 12 kacal gabanin zaɓen 2027.

Ana ganin Tinubu bai karya doka ba

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Me yasa gwamnoni 33 ke goyon bayan tazarcen Tinibu?

Sai dai George ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ko ƙa’idojin APC ba su fayyace yadda ɗan takarar shugaban ƙasa zai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe ko dabarun da zai yi amfani da su ba.

Ya ce:

“Har yanzu ban ga wani sashe a kundin tsarin mulki, dokar zaɓe da aka yi wa gyara, ko ƙa’idojin APC da ya ce dole ne ɗan takara ya ziyarci jihohi 36 kafin ya cancanci tsayawa takara, a zaɓe shi ko a sake zaɓensa ba.
“Haka kuma, babu wani abu a cikin waɗannan takardu da ya ce dole ne a yi muhawara. Duk waɗannan abubuwa sun danganta ne da dabarun ɗan takara.”

George ya ce Tinubu ya yi nazari kan taswirar zaɓe ta ƙasar, sannan ya yanke shawarar cewa ci gaba da riƙe nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin tattalin arziki shi ne babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin yakin neman zaben APC gabanin zaben 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

The Cable ta ce wani nazari kan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ta 2026 da ƙa’idojin yaƙin kamfe na INEC ya nuna babu wani sashe da ya fito ƙarara da ya wajabta wa ɗan takarar shugaban ƙasa gudanar zuwa kamfe a dukkan jihohi 36.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓen 2027, Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinoni 6 a INEC

Jihohi 12 da Tinubu ya ware

Kun ji cewa, shugaban Najeriya, Bola Tinubu , ya bayyana cewa zai fifita gudanar da mulki fiye da harkokin yaƙin neman zabe.

Shugaban kasar ya buƙaci shugabannin jam'iyyar APC da masu tsara kamfen su ɗauki nauyin wayar da kan magoya baya a jihohi da ƙananan hukumomi.

Duk da haka, an tsara cewa shugaban ƙasar zai halarci tarukan kamfen a birane 12 da ke shiyyoyin siyasa shida na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262